Sunday, 10 June 2018

Mataimakain Shugaban Kasa Ya Tsallake Rijiya Da Baya


anar Alhamis da ta wuce ne, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi

Osinbajo ya tsallake rijiya da baya,  yayin da jirgi mai saukar ungulu da yake ciki ya fara fitar da  hayaki.Hakan ya sanya aka tilastawa jirgin sauka a garin  Abuja kuma jirgin ya kai Yemi Osibanjo ne taro a kwalejin hukumar kwastam da ke Gwagwalada a cikin garin Abuja.

Osinbajo ya je kwalejin ne don halartar taron yaye manyan jami’an hukumar na wannan shekarar kuma dama jirgin ne ya kai Mataimakin wurin taron.

An ruwaito cewar, jirgin bai riga ya yi nisa da kasa ba, inda aka tilasata wa jirgin sauka bayan da ya fara fitar da hayaki, inda hakan ya sanya aka dauke mataimakin daga wurin ya tafi ta hanya

Ozil Ba Zai Buga Wa Jamus Gasar Cin Kofin Duniya

an wasan gaba na Arsenal, Mesut Ozil, ba zai samu damar bugawa kasarsa ta Jamus wasan cin kofin duniya ba, bayan raunin da ya samu yayin wani wasan sada zumunta da Austria ta lallasa su da ci 2 da 1 ranar asabar din da ta gabata. 


Haka zalika Ozil mai shekaru 29 a duniya ba zai buga wasan sada zumunci da Jamus ta kara da Saudi Arabia a ranar Alhamis ba.

A cewar shugaban tawagar kwallon kafar ta Jamus Oliver Bierhoff, dan wasan zai iya maleji ya doka wasannin cin kofin duniyar amma baya son takurawa lafiyarsa. Ozil, wanda ya kammala kakar wasa ta bana da rauni a baya, ya yi iyakar kokarinsa wajen ganin ya shiryawa gasar cin kofin duniyar wadda za su hadu da Medico a wasan farko ranar 17 ga watan nan kafin daga bisani su fafata da kasar Korea ta kudu da kuma kasar Sweden wadanda dukkaninsu ke a rukunin F. Tuni dai mai koyar day an wasan kasar, Joachim Low ya shiga tsaka mai wuya wajen ganin yam aye gurbin na Ozil wanda yana daya daga cikin manyan ‘yan wasan kasar da suka taimaka mata idan tana buga wasa. Kasar Jamus dai ita ce ta lashe gasar cin kofin duniya da aka buga a kasar Brazil shekaru hudu da suka gabata bayan sun doke kasar Argentina a wasan karshe daci 1-0 kuma a tarihi kasar tanada kofin na duniya guda hudu.


Sanata Marafa Ya Tallafa Wa ’Yan Gudun Hijira A Zamfara
A jiya ne Sanata mai wakiltar yankin Zamfara ta tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Kabiru Garba Marafa ya bayar da tallafi ga dimbin al’ummar da suke gudun hijira a garin Mada ta Jihar Zamfara.

Wannan tallafi da Sanata Marafa ya bayar da wannan tallafi ne domin tausaya al’ummar da suka tsinci kawunansu a cikin wannan mawuyacin hali na yin gudun hijira bayan ‘yan bindiga sun tarwatsa su a mabambantan garuruwansu dake sassan Jihar Zamfara.

Yayin gabatar da sakon tallafin, wakilin Sanata Marafa ya bayyanawa Sarkin Mada, da dandazon ‘yan gudun hijiran cewa, Sanata Marafa na cikin matukar damuwa dangane da halin da ‘yan gudun hijiran suke ciki. Wakilin nasa ya bayyana cewa, wannan sakon a matsayin somin tabi ne, kuma tallafin gaggawa domin a taimakawa ‘yan gudun hijiran da abin da za su ci. 

Sanata Marafa ya bayyana cewa, zai yi tattaki da kansa domin ya zo ya ziyarce su don ganin halin da suke ciki daga baya. Daga cikin dimbin kayan tallafin da Sanatan ya aikawa ‘yan gudun hijiran sun hada da buhunan Shinkafa, katon-katon din taliya, Man ja, Man gyada da sauransu.

A jawabinsa, Sarkin Mada ya bayyana godiyarsa ga Allah bisa samuwar Sanata Marafa a Jihar Zamfara. ya ce; “Muna godiya ga Allah (T) da ya halitto mana wannan bawan Allah a cikin Zamfara, shi ne Sanata Kabiru Marafa. Wannan jajircewa da yake yi da irin wannan tallafi da yake bayarwa, wannan ba shi bane karo na farko. ba sai a yankinsa kawai yake kai tallafi ba, a duk fadin jihar yake kai wa. Mun san yana iya kokarinsa. Duk wata ya kan aiko da tallafi nan. Muna godiya a madadin uwayen kasa na wannan yankin.”


Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Shugaban Kasa: Ya Shugaba, Me Ka Ke Tsoro Ne?Ya na cin zaben kujerar sanatan tsakiya a jihar Kogi ya fara kitsa makarkashiyarsa. Me ka ke tsammani daga mutumin da ya yi wa mahaifinsa makirci irin na siyasa? Sanin cewa sun goya ma ka baya wajen darewa mulkin kasar nan a shekarar 2015, Sanata Bukola Saraki da mukarrabansa sun kwana da sanin wane irin mutum ne kai, don haka sun shiga APC da shirinsu da kuma manufa. Gungun mutane ne wadanda sun fito daga jam’iyya mafi daurewa rashawa da cin hanci a tarihin siyasar kasar nan, don haka kudurinsu bai wuce na kare kansu daga barazanar da ka ke wakilta ba ta kare hakkin talaka da dakile rashawa da cin hanci. Sun gane cewa hanya daya da za su iya tsira cikin mulkinka shi ne hade kai da kwatar matsayi da zai iya ba su kariya. Wannan matsayi shi ne na shugaban majalisar dattijai. Sun yi gamon katar kasancewar ka zabi bin tsari na bawa kowanne bangaren masu mulki damar cin gashin kansa, inda ka zabi barin jam’iyyar APC ta shiga tsakani wajen zabo wanda zai dare wannan mahimmiyar kujera.

 Wannnan shi ne mafi girman kuskure da ka yi, domin yayin da su ka yaudare ka zuwa babban dakin taro na kasa-kasa da ke Abuja, tuni sun yi ma ka juyin mulki. Juyin mulki ma na tunda sun kaucewa bin tsarin jam’iyya wanda ya ba su kujerunsu su ka nada Bukola Saraki ba sahalewarka ballantana ta jam’iyya. Ka kawar da kai daga wannan zagon kasa, watakila domin tsoron kada a ce ka na mulkin kama-karya da kuma burinka na ganin ka jaddada doka da oda. 

Amma wannan ne kuskure mafi girma da ka yi shigowar ka mulki, kuma kuren da tun daga wannan rana kawo yanzu kai da talakawan kasar nan ke biya. Bari na kawo ma ka wasu daga cikin hujjojin da su ka sa na fadi haka. Lokacin da a ka fara maganar shari’ar Bukola Saraki a kotun da’ar ma’aikata, a rana ta farko ya sami rakiyar ’yan majalisa 83 daga cikin 103 da ke majalisar dattijai. Wadannan sanatoci sun yi dango domin kare rashawa da nuna su na tare da shi kasancewar kusan dukansu ja-ya-fado ne ja-ya-dauka. 

Da akwai kyautar majalisa mafi rashin kima a duniya na tabbatar da wannan majalisa ta takwas ta lashe gasar. Sakamakon alkalin ya nuna da gaske zai yi shari’ar, dattawan naka sai da su ka gayyace shi zaurensu. Bayan nan, hukumar kwastam ta kama motoci na alfarma wadanda ba a biya mu su haraji ba na shugaban majalisa, abinda ya sa majalisar ta gayyato shugaban kwastam, Hamid Ali, zuwa zaurenta, don nuna kin jinin yadda ya ke ayyukansa na ba-sani-ba-sabo. Sannan su ka matsa sai ya saka kayan aikin kwastam zai shiga zauren. Hamid Ali fa tsohon janar ne, wanda ya yi ritaya kuma mukaminsa ya fi na shugaban kwastam! Ina dalilin sai ya saka kayan sarki? 

Yayin da EFCC ta karkade fayil-fayil na sanataoci da a ke zargi kuma a ka gurfanar a gaban kotu, ciki har da shugaban majalisar, sai kawai su ka kada kugen yaki da shugaban EFCC, Ibrahim Magu, da kiraye-kirayen lallai sai ka cire shi, amma ka yi kememe, wanda sakamakon hakan su ka ki tabbatar da shi a mukaminsa a karo biyu da ya je gabansu. Na tuna cewa ba su bar kansu ba, domin daya daga cikin ’yan gaba-gaba wajen kitsa wancan juyin mulki da su ka yi ma ka, wato Ali Ndume, wanda a baya dan lelen saraki ne, amma sai ga shi sun cire shi daga mukaminsa sun dakatar da shi daga majalisa, saboda ya ja da Sarakin (Ina ganin alhaki ne ya kama shi ko?) Rigima tsakaninsu da kai ta dauki sabon salo a lokacin da ’yan sanda su ka nemi Dino Melaye ya kai kansa gabansu, saboda zarge-zarge da wasu daga cikin yaran da ya ke bawa makamai su ka fada hannun ’yan sanda. 

Dino ya ki amsa gayyatar har sai da ta kai sun cafke shi kuma ya tafka abin kunya da ya zubar da martabar majalisar dattijai da ma kasarmu gabadaya, domin nuna halayya tamkar irin ta ’yan dabar da su ka ce ya na da hannu a ayyukansu, sai ga shi ya nemi tserewa daga motar ’yan sanda lokacin da ta ke tafiya a kan titi. Kai shi kotu da kuma tsare shi a kurkuku ya jefa tsoro a zukatan su Bukola ganin cewa idan ka na sanata ba ka fi karfin doka ba. An kitsa wani makircin na kutsawa cikin majalisa da wasu ’yan daba yadda har su ka karbe sandar majalisa su ka fita da ita duk da cewa ginin majalisa na cikin wurare mafiya tsaro a fadin kasar nan, domin sai ka na da gayyata daga cikinta ko ka na aiki a ciki, sannan za ka iya shiga cikin ginin. Ina ganin an so a cigaba da kawo tsaiko ne a majalisa domin kada su sami damar sahale kasafin kudi da ke gabansu tsawon wata shida, don makarkashiya ga gwamnatinka. An yi fashi da makami mafi muni a tarihin Najeriya a garin Offa da rana tsaka, inda barayin su ka hallaka ’yan sanda tara da mutane sama da 38 ciki har da mace mai ciki a bankuna shida. Ashe wadannan gungun ’yan fashi yaran siyasa ne na Saraki, kuma bayan kwana biyu kacal da aika-aikar sai ga shi an gan su da Sarakin sun je gidan wani basarake yin jaje, saboda gwanintar makirci. A na cafke wadannan ’yan fashi da bincikarsu wanda ya sa babban sufeton ’yan sanda na kasa ya umarci a maida su Abuja. Jin haka sai gwamnan jihar Kwara ya sanar da Saraki abinda a ke ciki, shi kuwa Saraki ya na tuna abinda ya faru da Dino Melaye sai hantarsa ta duri ruwa. Nan da nan ya garzaya gabanka tare da gungun wasu ’yan majalisa, domin kai karar Sufeto Janar na ’yan sanda cewa ya na kitsa ma sa bi-ta-da-kulli. Ya’ilahi idan babu rami me ya kawo rami? Kamar yadda ka saba, ka ba su shawarar su bar doka ta yi aikinta a wanke mai gaskiya. Ciki da gaskiya kuwa ai wuka ba ta huda shi. Babban Sifeton ’yan sanda na mika wa Saraki gayyatar ya zo ya kare kansa, sai hankali ya tashi, domin ya san cewa fa alamun nesa ta zo kusa, don haka a nasa haukan gani ya ke mafita guda daya ta rage ma sa, wato ya kawo maganar a tsige ka. Watakila ya zunguro tsuliyar dodo, dodon da kuma zai hadiye shi da gungunsa, domin abinda ya yi tamkar kada kugen yaki ne a kan ’yan Najeriya. Kada mu manta nan ba da dadewa ba sanatoci da ’yan majalisar wakilai su ka hargitse lokacin da hukumar zabe ta fitar da jaddawalin zaben badi, kuma hantarsu ta duri ruwa, su ka kai gauro su ka kai mari, don ganin an canza jadawalin, amma su ka kasa samun yawan kuri’ar da za su iyi yin watsi da kudurin. Shin wadannan ne za su iya samun kuri’ar tsige ka? 

Abin dariya, yaro ya tsinci hakori! Ya Mai Girma Shugaban Kasa, na fahinci hikimarka ta barin tsarin doka ta yi aiki, domin idan hakan ya samu, ko ba ka nan, tsarin zai dore kuma a yanzu ma mun ga nasarar hakan, don kwanan nan mu ka ga kotu  ta tasa keyar Jolly Nyame kurkuku bayan fadi-tashi na kimanin shekaru 11. Sannu a hankali tsofaffin gwamnoni irinsu Shema, Shekarau, Lamido, Yero, Jang, Dariye, Goje, Kalu, Muazu da sauransu, za mu ziyarce su a kurkuku da gudunmuwar garin kwaki! 

To, amma duk da haka akwai lokaci fa na kawar da kai, akwai kuma lokaci na fuskantar abokin gaba, musamman idan da kansa ya buga kugen yaki. Na san a matsayinka na tsohon janar wanda ya jagoranci yaki ka san haka tun kafin a haife ni. Ba na manta kokarin halaka ka da makiya su ka yi, sai da ka shafe kusan shekara ka na jiyya, amma cikin hikimar Allah da addu’o’i da ka sha daga sassa na duniya Allah ya karba ya dawo ma na da kai har ka fi jiya kwari. 

Tun dawowar ka mu ke tsammanin tunda ka je bakin rami ka dawo, za ka zo ka fafari azzalumai ka garkame ma na su a kurkuku. Kash! amma sai ka ki. To, amma tunda yanzu su Bukola sun kalubalance ka gaba-da-gaba, mu na fatan ba za ka yi kasa a gwiwa ba. Wannan majalisa ta Takwas ba a taba mai muninta ba kuma tun da ta shigo ba ka jin komai daga cikinta sai yaki da gaskiya, saboda ba da Bukola Saraki kabai a ke yaki ba; shi ne dai jagora mai wakiltar dandazonsu. Yanzu dama ta samu, an sami shaidu kwarara na tuhumarsa. Don haka matukar ba a bincike shi an yanke ma sa hukunci ba, to yaki da rashawa da cin hanci da karya dokokin kasa ya yi nasara a kanka da kasarmu!


Mutanen da aka sace a Birnin Gwari na cikin hatsari


'Yan bindigar da suka sace mutum 25 a Birnin Gwari da ke jihar Kaduna a arewacin Najeriya sun bukaci a biya su miliyoyi kafin su sake su.
Mutanen da 'yan bindigar ke garkuwa da su, sun kunshi mata da ke shayarwa.
Wani mazauni Birnin Gwari kuma makusanci ga mijinta matar da ke shayarwa ya shaida BBC cewa 'yan bindigar sun bukaci a biya Naira miliyan biyar kafin su saki mutanen.
Ya ce sun kira mijin matar sun shaida masa adadin kudin da suke bukata. "Mijin ya yi ritaya daga aiki ba ya da karfin biyan kudin" in ji shi.
Ya ce akwai kuma 'yar uwan mijin da aka sace su tare da matarsa da ke shayarwa.
"Yanzu barayin sun amince a biya Naira miliyan daya ga duk mutum daya da kuma katin waya na Naira 30,000 kafin su sake su."
Ya kara da cewa sun tattauna da matan kuma sun ce duk ruwan da ake akansu yake karewa, kuma ba wani abincin da barayin ke ba su.
Tun a ranar Juma'a 'yan bindigar suka tare motocin fasinja a hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna kuma suka yi awon gaba da mutane dama da ke cikin motocin.
BBC ta yi kokarin jin ta bakin 'yan sanda amma kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ASP Aliyu Mukhtar bai amsa kiran waya ba.
Yankin Birnin Gwari a Kaduna na cikin yankunan arewa maso yammaci da ake yawan samun matsalar sace-sacen mutane domin kudin fansa.
Wata kungiyar tabbatar da tsaro da shugabanci na gari wato Birnin-Gwari Vanguards For Security and Good Governance ta yi kira ga gwamnati ta gaggauta tura jiragen yaki domin gano mabuyar 'yan bindigar da suka addabi yankin tare da tarwatsa su.
Kungiyar ta ce idan har ba a dauki mataki ba musamman a hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna da yankin Sabon-Birni da Maidaro da hanyar Birnin-Gwari zuwa Funtua da kuma dajin Kamuku, to mutanen yankin ba za su iya fita ba domin noman abincin da za su ci.

'Bom ya tashi da wasu yara a Adamawa'


Wani bom da wasu yara guda uku suka tsinta ya tashi da su a garin Mubi da ke cikin jihar Adamawa a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Daya daga cikin yaran ya mutu yayin da biyu suka samu mummunan rauni.
Al'amarin ya faru ne a ranar Lahadi a wani wurin da ake kira Filin Ajakuta inda ake tara karafa zuwa kudancin Najeriya.
Kwamishin watsa labaran jihar Adamawa Ahmad Sajo wanda ya tabbatar wa da Duniyar Yau da faruwar lamarin ya ce "ba harin bom ba ne ko harin kunar bakin wake."
"Wasu yara ne guda uku 'yan jari bola suka tsinci bom, sun yi tsammanin wani abu ne mai daraja da za su iya sayarwa su samu kudi." in ji shi.
Ya kara da cewa bom din ya fashe ne a lokacin da yaran suke kokarin sayarwa ga masu sayen kayan bola.
Ya ce mummunan raunin da yara biyu suka ji, ana tunanin sai an yanke wa dayansu kafa.
Jihar Adamawa na daya daga cikin jihohin arewa maso gabashin Najeriya da suka yi fama da rikicin Boko Haram.
Ana tunanin yaran sun tsinto abubuwan da aka ajiye, ba su fashe ba a rikicin Boko Haram.
Sajo ya ce zai iya kasancewa lokacin da ake gwagwarmaya da Boko Haram, mayakan suka bar shi har yaran suka tsinta suna tsammanin wani abu mai daraja ne su sayar don su samu kudi.
Ya ce an taba samun irin haka a garin Garkida inda wasu yara suka dauko bom daga daji suka kawo gida kuma ya fashe ya yi barna.
Yanzu haka dai ya ce jami'an tsaro na bin diddigin lamarin domin gano inda yaran suka tsinci bom din.
"Binciken jami'an tsaro ya tabbatar da cewa ba an yi amfani da yaran ba ne domin kai hari, illa yaran sun yi baban bola ne da nufin samun kudi" a cewar kwamishinan na watsa labarai.

Mawakin Reggae Ras Kimono ya mutu a Legas


Fitaccen mawakin na Reggae a Naijeriya, Ras kimono ya mutu a birnin Legas.
Rahotanni daga na kusa da 'yan uwan marigayin sun tabbatarwa da BBC cewa ya mutu a ranar Lahadi ne bayan ya yanke jiki ya fadi.
Ya kasance daya daga cikin kalilan da su ka kwaikwayi marigayi Bob Marley shekaru kadan bayan mutuwarsa a shekarar 1981.
Kungiyar makada da mawaka a Najeriya ta nuna kaduwarta da mutuwarsa.
Ras kimono a cikin wakarsa ta under pressure da yayi cikin shekarar 1980 ya nuna irin wahalhalun da ake ciki a Najeriya.

Daya daga cikin na kusa da shi ya fadawa BBC cewa marigayin da ke shirin ketarawa zuwa Amirka a jiya ya yanke jiki ya fadi, kuma nan take aka garzaya da shi wani asibiti a Ikeja.
Daga bisani aka mayar da shi asibitin Lagoon da ke Ikoyi har zuwa lokacin da ya cika a ranar Lahdi.
Daya daga cikin na kusa da shi ya ce, "In har labarin mutuwarsa ta zo mu ku da wasa to na zama daya daga abin nunawa a game da mutuwarsa. Lalle ya mutu."

A zamanin sa wakokin reggae sun samu karbuwa a Najeriya

Ras kimono dai ya yi tashe shekaru kadan bayan rasuwar Bob Marley a daidai lokacin da 'yan Rastafari ko Reggae ke neman wani da zai maye gurbi ko gaji Bob Marley a 1981.
Kuma ya yi tashe matuka ba kawai a Najeriya ba har ga sauran nahiyoyi, musamman a Afirka.
Ko da yake mawakin bai kasance wani da ya sha yin fito na fito da hukumomi kamar marigayi Fela Anikulapo Kuti a Najeriya ba - to amma akasari daga salon wakokinsa masu ratsa jiki ana alakanta su da lalubo hanyoyin warware matsalolin tsaro da talauci da danniya da shugabanni ke nunawa a Naijeriya.
Wasu daga wakokin sun janyo hankulin al'umma bisa kaunar juna da kuma nishadantarwa - saukin kan da marigayi Ras Kimono yake da shi ya sa ya dade akan ganiyarsa.
Da yawa daga mawakan Reggae dai ana alakanta su da shan tabar wiwi, wani abu da ba saban ba.
Marigayi Ras Kimono ya sha nanatawa cewa "Ba na shan taba bana shan wiwi kuma ni ba mai bin mata ba ne."
Daya daga cikin wakokinsa da 'yan Afirka ke matukar kauna ita ce ta "Ayaga yaga yaga yoh".
Yayi zamani da fitattun mawaka kamar Majek Fashek da Shina Peters da Wasiu Ayinde Barrister da Evi Edna Ogholi da dai sauransu.
Ya rasu yana da shekara sittin a duniya.
An haifi Ras Kimono a Asaba cikin jihar Delta a Najeriya, kuma ya mutu ya bar mace daya da 'ya'ya.

'Mijina mai shekara 84 ne ke yi min kwalliya'Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon yadda tsoho mai shekara 84 ke wa matarsa kwalliya:
Raunin ganin Mona ya na hanata iya yin kwalliya da kanta. Don haka mijinta Des mai shekara 84 ya koyi yadda ake yin kwalliya don matarsa ta yi kyau. Sun yi shekara 56 su na tare.

Neymar ya kamo Romario a cin kwallaye a Brazil

Neymar ya kamo Romario a cin kwallaye a Brazil
Neymar ya shiga sahun 'yan wasa uku na Brazil da suka fi yawan cin kwallaye a raga a kwallon kafa.
Dan wasan da ke taka leda a Paris Saint-Germain ya ci kwallonsa ta 55 a wasan sada zumunci da Brazil ta doke Austria 3-0 a ranar Lahadi.
Yanzu Naymar ya yi kafada da Romario wanda shi ma ya ci wa Brazil kwallaye 55, kuma na uku a jerin 'yan wasan kasar da suka fi zura kwallo a raga.
Pele ne kan gaba wanda ya ci wa Brazil kwallo 77 a raga, sai Ronaldo da ke bi masa da ya ci kwallo 62.
Karon farko ke nan da aka fara wasa da Neymar tun watan Fabrairu saboda raunin da ya yi fama da shi.
Gabriel Jesus da Philippe Coutinho ne suka ci wa Brazil sauran kwallayen a ragar Austria.
Wasan shi ne na karshe a shirye shiryen Brazil na zuwa gasar cin kofin duniya a Rasha.
Brazil wacce ta ci dukkanin wasanninta na share fagen gasar cin kofin duniya, za ta fara wasanta na rukuni ne da Switzerland a ranar 17 ga watan Yuni kafin ta hadu da Costa Rica da kuma Serbia.
Brazil za ta tafi Rasha da haushin kashin da ta sha hannun Jamus ci 7-1 a gasar cin kofin duniya da ta karbi bakunci a 2014.

Daliban Shari'a sun yi jarabawa a kan Ramos da Salah

Daliban Shari'a sun yi jarabawa a kan Ramos da Salah

Gumurzun da ya tursasa wa Mohamed Salah ficewa fili yana kuka a minti 30 a wasan karshe na gasar Zakarun Turai ya fito a jarabawar nazarin ilimin shari'a, kamar yadda aka ruwaito.
Hoton takardar jarabawar ta dalibai 'yan shekarar farko a jami'ar Damascus, ya mamaye shafukan Facebook na Syria.
An tambayi daliban cewar: "Sergio Ramos ya raunata Mohamed Salah a wasan karshe na lashe kofin Zakarun Turai.
"A bisa tsari, ba za a iya kama Ramos da laifin da ya aikata ba a dokar aikata laifuka ba, saboda wasu sharudda guda hudu da suka shafi rikici a wasanni. Fadi wadannan sharuddan."
Tambayar kamar an gamu ne da an dace musamman hamayyar wasan kwallon kafa da ke tsakanin daliban, yayin da wani shafin intanet na Enab Baladi da ke adawa ya bayyana malamin da ya shirya tambayar a matsayin "Dan Barcelona da ya sha kashi."
Real Madrid abokiyar hamayyar Barcelona dai ta lashe kofin gasar a Kiev bayan ta doke Liverpool 3-1.
Wani ya yi tsokaci a Facebook cewa: Duk wani magoyi bayan Barcelona zai yaga takardar jarabawar kuma ya fice bayan ya ji an ambaci sunan Ramos."
Wasu kuma sun yabi Farfesan da ya rubuta tambayar musamman ga daliban domin amfani da dokokin shari'a a wani abun da ya faru a zahiri.
Shafin Facebook na Jami'ar ya fitar da sanarwar da ke kare malamin. "Babu sarkakiya a Tambayar, dukkan godiya ga malamai baki daya."
Sanarwar ta kuma wallafa hoton tambayar, da kuma amsa, kuma wani dalibi ya amsa tambayar daidai kamar yadda shafin facebook na kafar Hawa TV ya wallafa
Amsar Sharudda guda hudu da aka tambayi daliban da aka wallafa su ne:
1 - An yi wasan ne a bisa doka.
2 - Dan wasan wanda ya ji rauni, ya amince ne ya buga wasan.
3 - Dan wasan da ya yi dalilin raunin, ya san dokoki da sharuddan wasan.
4 - Ga raunin da aka samu a lokacin wasan.

An rushe Hukumar Kwallon Kafa ta Ghana

An rushe Hukumar Kwallon Kafa ta Ghana

Gwamnatin Ghana ta rusa hukumar Kwallon Kafa ta kasar bayan da aka dauki bidiyon shugaban kungiyar yana karbar "na goro".

An dauki bidiyon Kwesi Nyantakyi yana karban dala 65,000 daga wani dan jarida mai binciken kwakwaf wanda yayi bad-da-kama, inda ya ce shi dan kasuwa ne mai sha'awar zuba jari a wasannin kwallon kafar kasar.

Sai dai kawo yanzu bai ce uffan game da tuhumar da ake masa.

Ministan wasanni na Ghana, Isaac Asiama ya ce an "rusa hukumar take-yanke", kamar yadda jaridar GhanaWeb ta ruwaito.

Manema labarai sun ce wannan tonon sililin aikin dan jaridar nan ne dan asalin kasar Ghana mai suna Anas Aremayaw Anas, wanda a sanadiyyar aikin nasa ya bankado ainihin badakalar da ake yi a fagen kwallon kafa a nahiyar Afirka.

A watan jiya aka mika wa hukumomin kasar fim din da ya hada mai suna "When Greed and Corruption Become the Norm", wato lokacin da hadama da rashawa suka zama jiki.

Ranar Laraba kuma aka nuna fim din a ko'ina cikin kasar da ma duniya.
Wednesday, 30 May 2018

Yadda 'yan sanda suka tarwatsa magoya bayan Shekarau

Wani Matashi Ya Kera Wata Fanka Mai Samar Da Wutar Lantarki Wato Wind Turbine a Turance

Kalli Wata Fanka Mai Samar Da Wutar Lantarki Wato Wind Turbine a Turance Da Wani Matashi Ya Kera


Kalli video kai tsaye

Hotunan yadda Musulmin Amurka suka sha ruwa

Hotunan yadda iska mai karfi ta lalata fiye da gidaje 100 a Argungu
TALLA

Talla