wasanni
Dalilin da ya sa ba zan iya auren ’yar Najeriya ba – Kocin Eagles Gernot Rohr
Kocin kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles Gernot Rohr ya bayyana dalilan da za su sa ba zai iya auren wata mace a Najeriya ba.
A wata tattaunawa da ya yi da jaridar Turanci ta The Sun a karshen makon jiya, kocin ya ce a gaskiya ba zai iya auren wata mace a Najeriya ba saboda bambancin al’ada da kuma yare.
Da aka tunatar da shi game da yadda tsohon kocin Eagles Clemens Weterhof dan asalin Holand ya auri ’yar asalin Zimbabwe a lokacin da yake horarwa a can, Gernot Rohr ya ce shi ba zai iya yin haka ba. Ya ce saboda matsalar yare da kuma ta al’ada ba zai iya yin aure a Najeriya ko a Afirka ba,
Ya ce a kwanakin baya ma sai da shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya Amaju Pinnick ya zolaye shi a kan ya auri ’yar Najeriya amma da yake raha yake yi, sai suka kwashe da dariya, kuma a nan maganar ta mutu.
“Da son samu ne, da na yi aure a Najeriya, amma ganin yadda muke da bambancin al’ada da na yare, ba na tunanin zan iya auren wata mace a Najeriya”, inji shi.
“A gaskiya matan Najeriya na da kyau amma babbar matsalar ita ce ba zan iya auren daya daga cikinsu ba saboda bambancin al’ada da na yare.”
Gernot Rohr wanda dan asalin Jamus ne ya fara horar da kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ne a shekarar 2016 bayan Sunday Oliseh ya ajiye mukamin koci. Sannan ya horar a kasashen Afirka da dama kafin ya zo Najeriya ciki har da Gabon a tsakanin shekarar 2010 zuwa 2012 da Nijar a tsakanin shekarar 2012 zuwa 2014 sai Burkina Faso a shekarar 2015 kafin ya koma Najeriya a shekarar 2016.
0 Comments: