Headlines
Loading...
Ramadan: Abu shida da ake samun sabani a kansu kan azumi

Ramadan: Abu shida da ake samun sabani a kansu kan azumi

Musulmai a fadin duniya na ci gaba da azumtar watan Ramadan mai tsarki, inda ake so su kame bakinsu daga ci da sha da kuma kiyaye dokokin Allah tun daga ketowar alfijir har zuwa faduwar rana.

Manufar ita ce habaka imani da tsoron Allah, da kiyaye addini ta hanyar yin addu'o'i da kamun kai, saboda watan Ramadan yana ba da damar kara tsoron Allah. 

Duk da cewa a zahiri batun da ya shafi dokokin azumi abu ne mai saukin fahimta, amma akwai abubuwa kadan da akan samu rarrabuwar kawuna a kai tsawon shekaru. 

A mafi yawancin al'amura ana dogara ne a kan mazhabobi, kuma wasu daga cikin abubuwan da za mu zayyano a kasa sun danganta ne da yadda aka fassara su.

Ga shida daga ciki kamar yadda wani Malamin addinin musulunci a Gabas Ta Tsakiya Shabbir Hassan, kuma mahaddacin Kur'ani ya fayyace:

Yin burushi yana karya azumi?

Mafi yawan malamai sun yi ittifakin cewa yin burushi ba ya karya azumi.

Malam Hassan ya ce wasu lokuttan idan masu azumi suka ji dandanon man wanke baki ko da dan kadan ne a bakinsu, sai su ga tamkar ya isa ya karya musu azumi.

Duk da cewa malamai da dama sun yarda cewa za a iya yin burushi, Malam Hassan ya ba da wasu shawarwari ga masu yin taka tsan-tsan.

"Shawara mafi kyau ita ce a yi amfani da man wanke baki kadan - wanda kuma ba shi da karfi. Ya kuma ba da shawarar yin amfani da asuwaki - kasancewar ba shi da wani dandano na daban. Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayar da shawarar yawaita amfani da asuwaki don tsabtace baki.

Zaka iya hadiye yawunka?
Babu laifi ga mai azumi ya hadiye yawunsa, kamar yadda kusan dukkan malamai suka yarda a kai, ana kuma karfafa wa mutane gwiwar yin hakan sosai. 

Malam Hassan ya ce: "Babu wata tababa a kan batun hadiye yawu ga mai azumi, hadiyar yawu abu ne da yake tamkar jini da jiki, ba za a iya cewa ma za a daina ba. Babu shakka ba ya karya azumi."
Abun da ke karya azumi shi ne kawai idan hadiyar yawun ya kasance tsakanin naka da na wani ne, kamar sumba. 

Hadiye yawun wani daban, abu ne da yake da dan bambanci da hadiye yawunka, kuma ya kamata a guje masa yayin da aka dauki azumi," in ji Malam Hassan. "Bai halatta a yi sumba ko tarawa ba. Makasudin yin azumi shi ne tabbatar da rike sha'awarku ta abinci da abun sha da kuma saduwa da iyali."

Ci da sha kawai aka hana?

Ana kuma so mai azumi ya bar gulma da karya
Ba ci da sha ne kawai ayyukan da ke bata azumi ba. Sauran dokokin azumi sun hada da rike harshe daga aikata sabo. "Gulma da karya da zagin mutane na daga cikin abubuwan da za su iya bata azumi, in ji shi.

Ko ci da sha bisa kuskure na karya azumi?

dan kuka ci ko shan wani abu bisa kuskure to azumi yana nan, muddun mutum ya daina cin abincin da zaran ya tuna. 

Idan ka hadiye ruwa wajen alwala da gangan, azumi ya karye. Amma idan ba da gangan ba ne, mafi yawancin malamai sun yadda azumin ka iggantacce ne.

Ko za a iya shan magani ko allura?

"Idan kana da wata rashin lafiya to abu na farko da za ka tambaya shi ne ko akwai bukatar na yi azumi?"


Majalisar Musulmi ta Birtaniya (MCB) tare da hadin gwiwar Kungiyar masu yaki da cutar ido ta Glaucoma, sun fitar da wata sanarwa inda suka nemi mutane su ci gaba da amfani da wasu magunguna kamar na ciwon ido a yayin da suke azumi.

MCB ta bayar da wata takardar kula da lafiya lokacin Ramadan, wadda aka yi don amfanin asibiti, da ke nuna cewa maganin ciwon ido da kunne da allura, suna daga cikin magunguna da ba su karya azumi.

Amma, shan magani na hadiya yana bata azumi, saboda haka a rinka shan magani kafin alfijir ko bayan shan ruwa.

Malam Hassan ya ce: "Da farko dai, idan kana fama da wata rashin lafiya ko cuta, abu na farko da za ka tambaya shi ne, shin cutar za ta iya barinka kai yi azumi ba tare da damuwa ba?

"Abin da ke bayyane karara a Alkur'ani shi ne cewa ya kamata a bi shawarar likita ko yaushe," in ji shi.

Shin wajibi ne a yi azumi a ko wanne irin yanayi?

Mutanen da suka tsufa tukuf na daga cikin wadanda aka dauke wa yin azumi
A musulunce, azumi ya zama wajibi ne kawai ga wadanda suke da lafiya kuma ga wadanda suka balaga. Azumi bai wajaba ba a kan kananan yara da ba su balaga ba, sai dai a kan so a dinga koya musu don su saba. Cibiyar MCB ta yi karin bayani cewa bai wajabta a kan marar lafiya ko mai lalurar tabin hankali ba, ko masu rauni ko matafiya ko masu ciki ko masu shayarwa. Sai dai daga cikin wadannan mutane akwai wadanda za su rama daga baya, akwai kuma wadanda musulunci ya dauke musu ramuwa, amma za su ciyar. Akwai wasu hanyoyin da wadanda ba za su iya azumin ba kwata-kwata za su bi su samu lada ba tare da asarar garabasar watan ba. "Idan akwai rashin lafiya ta gajeren lokaci da suka san za a warke - to za su rama azumin daga baya," in ji Malam Hassan.

"Idan kuma ciwo ne da zai hana su yin azumi kwata-kwata kuma likitoci sun tabbatar ba ranar warkewa, to sai su yi fidyah - wato ciyar da miskini a ko wacce rana.

0 Comments: