Headlines
Loading...
A shirye nake in dakatar da shirin nukiliya bayan ganawa da Trump – Shugaban Koriya ta Arewa

A shirye nake in dakatar da shirin nukiliya bayan ganawa da Trump – Shugaban Koriya ta Arewa

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un ya bayyana cewa a shirye yake ya ajiye shirinsa na mallakar makamin nukiliya matukar kasar Amurka za ta dauki alkawarin ba za ta kai masa hari ba.
Kim ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da takwaransa na kasar Koriya ta Kudu Moon Jae a wani taron koli da ya wakana tsakanin kasashen guda biyu.
Wannan itace babbar alamar da ke nuna shugaban Korea ta Arewar ya kukuri aniyar ganawa da shugaban na Amurka.
Shi dai shugaban Amurka Donald Trump ya tabbatar da cewa zai gana da shugaban na Koriya ta Arewa a cikin Mayu, amma kuma babu karin haske a kan abin da za a tattauna da kuma takamaiman lokacin da za a gana.
Hakanan kuma shugaba Kim ya yi alkawarin rufe sansanin gwajin makamin nukiliyarsa da ke kasar a watan nan na Mayu, kamar yadda ya bayyana wa masana da manema labarai daga kasashen Koriya ta Kudu da Amurka.
A daidai lokacin da ake tai komo da jiran tsammanin ganin ranar da shugaban Koriya ta Arewa zai cika alkawarinsa na dakatar da shirinsa na mallakar makamin nukiliya, wanda ake tunanin zai zama bayan ganawarsa ne da shugaban Amurka Donald Trump, wasu bayanan Kim din suna nuni da cewa yana tsoron sadaukar da makamansa baki daya.
Babban mai bada shawara kan harkokin tsaron kasar Amurka John Bolton, ya mayar da martani a game da maganar shugaban Koriya ta Arewa na cewa zai dakatar da shirinsa ne idan Amurka ta yi alkawarin ba za ta kai masa hari ba, inda ya ce, “Mun dade muna jin irin wannan maganganun. Koriya ta Arewa ta saba irin wannan farfagandar. Abin da muke so mu gani shi ne mu tabbatar da cewa za gaske suke yi ba wai shirirta ba,” inji shi.
… Zan so mu gana ne a yankin DMZ- Trump
A nasa vangaren, Shugaban Amurka ya ce a shirye yake ya gana da shugaba Kim na Koriya ta Arewa, sannan ya ce yana so su gana ne a yankin nan da ake kira DMZ da ke tsakanin kasar Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu, inda a nan shugaban Koriyan guda biyu suka gana.  
Amma kuma Trump ya ce kasar Singapore ta nuna sha’awarta na ganin an gudanar da taron ka kasarta, domin ta kafa tarihin cewa a kasarta ne aka dakatar da batun nukiliya da kuma samar da zaman lafiya tsakanin Amurka da Koriya ta Arewa. 
“Ina so mu gana ne a can ta yadda idan aka samu matsaya akwai biki mai girma wanda ya fi kamata a yi a kasashen ba a water kasar ba daban,” inji Trump.
kasashen da yawa a yankin Turai da Asiya da wasu kasashen da dama sun nuna sha’awar ganin sun dauki nauyin gudanar da ganawar a kasashensu, amma dai yanzu shugaba Trump ya sanyaya maganar bayan na nuna sha’awarsa na gudanar da ganawar a yankin Koriya.
Wannan ganawar dai za ta zo ne bayan shugabannin Koriyan gudan biyu sun gana da juna a makon jiya, inda suka dauki alkawarin kawo karshen rikici tsakanin kasashen guda biyu da ya ki ya ki cinyewa. 

0 Comments: