Headlines
Loading...
Soja Ya Harbe Jami’in Kwastam A Legas

Soja Ya Harbe Jami’in Kwastam A Legas

Soja Ya Harbe Jami’in Kwastam A Legas

Wani jami’in Hukumar Kwastam ya yi gamo da ajalinsa yayin da wani soja ya harbe shi a iyakar kan tudu ta Seme da ke Jihar Legas.


Wani ganau ya shaida cewar lamarin ya faru ne ranar Laraba da daddare.


“Da yiwuwar sojan yana cikin maye ne na barasa don babu wanda ya taba tsammanin zai yi aikata wannan barna da ba a san shi da ita ba,” a cewarsa.


Seme yanki ne na kasar Najeriya da ke iyaka da Kwatano, babban birnin Jamhuriyyar Benin.

0 Comments: