Headlines
Loading...
Ozil Ba Zai Buga Wa Jamus Gasar Cin Kofin Duniya

Ozil Ba Zai Buga Wa Jamus Gasar Cin Kofin Duniya

an wasan gaba na Arsenal, Mesut Ozil, ba zai samu damar bugawa kasarsa ta Jamus wasan cin kofin duniya ba, bayan raunin da ya samu yayin wani wasan sada zumunta da Austria ta lallasa su da ci 2 da 1 ranar asabar din da ta gabata. 


Haka zalika Ozil mai shekaru 29 a duniya ba zai buga wasan sada zumunci da Jamus ta kara da Saudi Arabia a ranar Alhamis ba.

A cewar shugaban tawagar kwallon kafar ta Jamus Oliver Bierhoff, dan wasan zai iya maleji ya doka wasannin cin kofin duniyar amma baya son takurawa lafiyarsa. Ozil, wanda ya kammala kakar wasa ta bana da rauni a baya, ya yi iyakar kokarinsa wajen ganin ya shiryawa gasar cin kofin duniyar wadda za su hadu da Medico a wasan farko ranar 17 ga watan nan kafin daga bisani su fafata da kasar Korea ta kudu da kuma kasar Sweden wadanda dukkaninsu ke a rukunin F. 



Tuni dai mai koyar day an wasan kasar, Joachim Low ya shiga tsaka mai wuya wajen ganin yam aye gurbin na Ozil wanda yana daya daga cikin manyan ‘yan wasan kasar da suka taimaka mata idan tana buga wasa. Kasar Jamus dai ita ce ta lashe gasar cin kofin duniya da aka buga a kasar Brazil shekaru hudu da suka gabata bayan sun doke kasar Argentina a wasan karshe daci 1-0 kuma a tarihi kasar tanada kofin na duniya guda hudu.


0 Comments: