Labaran Yau
Shugaban Karamar Hukuma Ya Cire Hakorin Kwamishiniya A Adamawa
Kwamishiniyar ma’aikatar albarkatun kasa ta jihar Adamawa Misis Shanti Sashi, ta maka shugaban karamar hukumar Lamurde Mista Barati Nzonzo a kotu, biyo bayan marin da ya wanka mata wanda ya yi sanadin cire mata hakori. Misis Sashi, ta maka shugaban karamar hukumar Lamurde a kotu ne kan batutuwa bakwai da suka shafi aikata munanan laifuka, ta kuma zargi shugaban da ci mata mutunci da azaba mai tsanani, da ya kai ta ga rasa hakora To sai dai lokacin da aka kira shari’ar gaban wata kotun majistare a ranar juma’ar da ta gabata a Yola, wanda ake zargin ya ki halartar zaman kotun.
Lauyar dake tsaya wa wacce ta kawo kara, Misis Mfoniso Gabriel, ta bukaci kotun da ta yi amfani da sashi na 154 karamin sashi na 1, na kundin tsarin dokar masu aikata miyagun ayyuka (CPC) ta bada umurnin kamo wanda ake zargin.
Shi kuwa Mista Jerry Ifegwu, lauya da ke kare wanda ake zargin ya ce, batun amfani da wacce dokar bai taso ba, domin wanda yake karewa bai bayyana a kotun ba. Ya ce duk da wanda yake karewa bai bayyana a kuton ba, amma ya samu labarin wasu manoma sun kai hari kan wasu kauyuka a karamar hukumar Lamurde, lamarin da ya tilasta mishi tafiya yankin a matsayinsa na babban jami’in tsaro a can.
Mista Ifegwu, ya bukaci shugabar kotun mijistari Misis Momsiri Bamare, da ta yi watsi da batun bada umurnin kamo, da ta bada umurnin mika duk takardun tuhuma ga lauyan wanda ake zargin. Yanzu haka dai shugabar kotun Momsiri Bamare, ta dage sauraron shari’ar zuwa 25/5/2018, domin ci gaba da sauraro.
0 Comments: