Headlines
Loading...
Ma’aikacin KASTELIA ya kwada wa daliba karfe a goshi

Ma’aikacin KASTELIA ya kwada wa daliba karfe a goshi


Ana zargin wani ma’aikacin Hukumar Kula da Hanyoyi da Tsabtace Muhalli ta Jihar Kaduna KASTELIA ya kwada wa wata daliba karfe a goshi har ta suma a yayin da suke gudanar da aikin kama masu ababen hawa a Zariya bayan da gwamnatin jihar ta umarci ma’aikatan hukumar su tabbatar da dokar hana haya da babura ko daukar fasinjoji fiye da kima a kan ababen hawa.

A ranar Alhamis din makon jiya ne ma’aikacin hukumar ya kwada wa dalibar mai suna Maryam Hassan mai kimanin shekara 13 karfen yayin da ma’aikatan suke kokarin tare Keke NAPEP din da ya dauko daliban, kan zargin ya dauko fasinja fiye da kima, inda ta fado kasa ta suma.

Aminiya ta ziyarci Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika inda ta tarar da ma’aikatan Hukuma KASTELIA na kaiwa da komowa tare da likitoci domin ceto ran dalibar da ke kwance a gadon asibiti. Kuma kokarin da wakilinmu ya yi don jin ta bakin dalibar bai samu nasara ba saboda halin da take ciki.


Malamin dalibar wanda shi ne ya sanya daliba a cikin Keke NAPEP din da kuma lamarin ya faru a kan idonsa mai suna Sa’idu Ma’azu, ya ce sun fito ne daga makaranta domin su ziyarci Asibitin Jama’atu Nasril Islam da ke kofar Fada, Zariya domin koyon sanin makaman aiki. “Ni ina kan babur ina gaba suna biye da ni, muna kawowa daidai Makarantar Alhudahuda inda ’yan KASTELIA suke tsayawa, sai suka yi kokarin tsai da direban Keke NAPEP din amma ya ki tsayawa, daga nan sai ma’aikatan suka bi su a guje, daya daga cikinsu yana rike da wani karfe a hannunsa, sai ya kai wa direban duka da karfen bai same shi ba sai ya samu dalibar tawa da karfen mai kama da kaca a goshinta. Nan take ta fado daga Keke NAPEP din ta suma, kuma goshinta ya yi wani katon rami a inda ya buga mata karfen, kuma jini ya roka fita ta baki da hanci da kunnenta,” inji shi. 


Malamin ya ce, ganin haka sai ’yan KASTELIA suka yi maza suka dauko mota aka kai ta wani asibiti, suka ce ba za su iya ba, sai aka kai ta asibitin Shika.


Mahaifiyar dalibar mai suna Sakina ta ce bayan sun tafi makaranta ita da wata da take riko da kawarsu daga makwabta sai ga su a rude cewa ta zo Maryam ta fado daga Keken NAPEP wani dan KASTELIA ya fasa mata goshi da wani karfe har ta suma. “Ina zuwa sai na ga ma’aikatan suna kokarin kai ta asibiti shi ne muka tafi tare, amma direban Keke NAPEP din yana tsare a hannun ’yan sanda,” inji ta.


Mahaifiyar Maryam ta ce, ba direban Keke NAPEP din kawai ya kamata a kama ba, har wadanda suka jawo hadarin, domin a matsayinsu na masu kula da kare lafiyar jama’a bai kamata a ce sun bi su da gudu ba, domin ba su san abin da zai faru da su ba. Ta ce yanzu ga yadda jini ke fita ta hanci da baki da kunnen ’yarta.


Wani babban jami’in da Aminiya ta iske a asibitin wanda ya ce shi ne mataimakin babban jami’in hukumar a shiyya ta daya da ke Kwangila, Zariya, mai suna Muhammed Sani ya ce wani ma’aikacinsu da ke da ke kula da karamin ofishinmu da ke cikin garin Zariya ne ya kira shi cewa sun samu hadari a wurinsu da wani mai Keke NAPEP da aka nemi ya tsaya ya ki kan ya dauki fasinja fiye da kima. Ya ce ya yi kan mutanensu a kokarinsa na ya gudu, sai daya daga cikin ma’aikatans da ke rike da wani abu da suke kulle tayar mota da shi ya kai duka sai ya samu yarinyar a kai ta fado har ta suma.

“Sai na yi maza na tura musu motarmu ta daukar marasa lafiya domin a kai ta asibiti, ni kuma na biyo su domin in ga halin da take ciki, kuma kusan duk abin da ake bukata a asibitin ni ke daukar nauyi, kuma shi mai Keke NAPEP an kama shi shi ma’aikacin namu da aka ce shi ne ya ji wa yariyar rauni na ce a tsare shi. Yanzu abin da muke kokari shi ne yariyar ta samu lafiya tukunna,” inji shi. 

Game da korafe-korafen da jama’a ke yi kan yadda jami’an hukumar ke gudanar da aikinsu na rashin tsari da cin zarafi, ya ce “Eh muna iyakar kokarinmu wajen fadakar da su da nuna musu yadda ya kamata su rika aikinsu, amma da yawansu suna da karancin sanin yadda ake gudananr da aiki, kuma mun fahimci wadansu daga cikinsu ba su da cikakken ilimin da ya kamata su ci gaba da gudanar da aikin, muna shirin tacewa a hankali ta yadda ba za a rika samun irin wannan matsala a tsakanin hukumar da masu ababen hawa ba.”    


A ofishin ’yan sanda da ke kofar Fada, Zariya, babban jami’insu Kasim Abdul ya ce sun kama mai Keke NAPEP din kuma ya aika da jami’ansa su kamo ma’aikacin Hukumar KASTELIA din domin dukansu masu laifi ne, kuma ya tura jami’ansa asibitin domin su ga halin da dalibar take ciki kafin daukar mataki na gaba.

0 Comments: