![Gwamnatin Najeriya ta dakatar da shafin Twitter a Najeriya](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEgWmOyEkPewGSEUMf6E7khWnVR_Li4YAd_yyalgj3PDLiF0qdJ9xLH_h_a4iwfZzUFoHyPa24kWK3kSnUfIlDju4D8Eoz3v2fZGCyUSK3yZJX4-5MjtzCDxke69QsgDQGpyfaxP_V22GGMd/w700/hoton-twitter.png)
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da ayyukan shafin zauren sada zumunta na Twitter a Najeriya.
Hakan na kunshe cikin wata sanarwa da Ministan Labarai da Al’adu na Kasar, Alhaji Lai Mohammed ya fitar a ranar Juma’a.
Sanarwar ta ce ana ribatar shafin na Twitter wajen kawo rabuwar kai a kasar nan.
Wannan mataki na zuwa ne kwanaki kadan bayan da shafin Twitter ya goge wani sakon gargadin ‘yan awaraen IPOB da Shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa.
0 Comments: