Headlines
Loading...
SERAP ta ɓukaci Sadiya ta yi bayani kan yadda za ta raba kuɗi ga talakawa

SERAP ta ɓukaci Sadiya ta yi bayani kan yadda za ta raba kuɗi ga talakawa

SERAP ta ɓukaci Sadiya ta yi bayani kan yadda za ta raba kuɗi ga talakawa

Kungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci a Najeriya ta buƙaci gwamnatin Najeriya ta yi bayani kan tsarin biyan kuɗaɗen da take raba wa talakawa.


Ƙungiyar ta ba ministar ma’aikatar kula da ayyukan jin-ƙai da kare Afkuwar Bala'i wa’adin mako ɗaya ta bayyana yadda ake shirin raba naira biliyan 729 ga ƴan Najeriya sama da miliyan 24.


Ƙungiyar ta ce tana son a yi mata bayani kan hanyoyin da za a bi wajen biyan kuɗin da sunayen waɗanda za su ci gajiyar shirin da kuma tsarin zaɓen mutanen da za a raba wa kuɗaɗen.


Kuma ko za a miƙa kuɗaɗen ne kai-tsaye ga mutane ko ta asusun banki.


SERAP kuma na son gwamnatin Najeriya ta yi bayani kan dalilin biyan N5,000 ga ƴan Najeriya miliyan 24.3, wanda ta ce ya yi daidai da kashi biyar cikin 100 na kasafin kuɗin Najeriya na 2021 na tiriliyan 13.6.


Zuwa yanzu babu wani martani da ya fito daga ministar ko ma’aikatarta da ke kula da raba kuɗaɗen ko kuma daga gwamnatin Najeriya.


SERAP ta yi gargadin cewa idan har ba ta ji komi daga gwamnati ba za ta ɗauki matakin shari’a ƙarƙashin dokar ƴancin samun bayanai don tilasta wa gwamnati yin abin da ta nema.0 Comments: