![Hotunan yadda Musulmin Amurka suka sha ruwa](https://blogger.googleusercontent.com/img/b/R29vZ2xl/AVvXsEin6G_LpHEKRk-0vnOelf4pXB4a8ngJ1JOeyBNzzR826vRckFZlK9R0Tko6j7PJvEVX707dpxtaSww041DhHKfPzsCK6MqSNX8KTyPmfatd7yG-5PJ9pFP2EInJePn_K7Cn5ffujzv0MnHN/w700/1.jpg)
BBC ta tattaro muku hotunan yadda wadansu Musulmi da ke kasar Amurka suka yi buda baki a ci gaba da azumin watan Ramadan.
Wani Musulmi lokacin da yake shan ruwa bayan faduwar rana a brinin New York na kasar Amurka ranar Laraba
Wadansu masu fafutika lokacin
suke buda baki da wata kungiyar 'yan ci rani ta shirya a birnin New
York na kasar Amurka ranar Laraba
Musulmi a Amurka suna kwashe kimanin sa'o'i 15 zuwa 16 na azumi wato tsakanin sahur da buda baki
Wata Musulma lokacin da take raba dabino a birnin New York ranar Laraba
Wadansu mata yayin da suke cin abinci bayan shan ruwa a birnin New York na kasar Amurka ranar Talata
Wadansu Musulmi mata lokacin da suke buda baki a cibiyar raya al'adu ta Eyup Sultan a birnin New York a makon jiya
Wadansu Musulmi lokacin buda baki a cibiyar addinin Karbala a jihar Michigan da ke Amurka ranar Juma'a
Jihar Michigan ita ce ta fi kowa ce jiha a kasar Amurka yawan Musulmi wadanda suka fito daga yankin Gabas Tsakiya
0 Comments: