Headlines
Loading...
Mawakin Reggae Ras Kimono ya mutu a Legas

Mawakin Reggae Ras Kimono ya mutu a Legas


Fitaccen mawakin na Reggae a Naijeriya, Ras kimono ya mutu a birnin Legas.
Rahotanni daga na kusa da 'yan uwan marigayin sun tabbatarwa da BBC cewa ya mutu a ranar Lahadi ne bayan ya yanke jiki ya fadi.
Ya kasance daya daga cikin kalilan da su ka kwaikwayi marigayi Bob Marley shekaru kadan bayan mutuwarsa a shekarar 1981.
Kungiyar makada da mawaka a Najeriya ta nuna kaduwarta da mutuwarsa.
Ras kimono a cikin wakarsa ta under pressure da yayi cikin shekarar 1980 ya nuna irin wahalhalun da ake ciki a Najeriya.

Daya daga cikin na kusa da shi ya fadawa BBC cewa marigayin da ke shirin ketarawa zuwa Amirka a jiya ya yanke jiki ya fadi, kuma nan take aka garzaya da shi wani asibiti a Ikeja.
Daga bisani aka mayar da shi asibitin Lagoon da ke Ikoyi har zuwa lokacin da ya cika a ranar Lahdi.
Daya daga cikin na kusa da shi ya ce, "In har labarin mutuwarsa ta zo mu ku da wasa to na zama daya daga abin nunawa a game da mutuwarsa. Lalle ya mutu."

A zamanin sa wakokin reggae sun samu karbuwa a Najeriya

Ras kimono dai ya yi tashe shekaru kadan bayan rasuwar Bob Marley a daidai lokacin da 'yan Rastafari ko Reggae ke neman wani da zai maye gurbi ko gaji Bob Marley a 1981.
Kuma ya yi tashe matuka ba kawai a Najeriya ba har ga sauran nahiyoyi, musamman a Afirka.
Ko da yake mawakin bai kasance wani da ya sha yin fito na fito da hukumomi kamar marigayi Fela Anikulapo Kuti a Najeriya ba - to amma akasari daga salon wakokinsa masu ratsa jiki ana alakanta su da lalubo hanyoyin warware matsalolin tsaro da talauci da danniya da shugabanni ke nunawa a Naijeriya.
Wasu daga wakokin sun janyo hankulin al'umma bisa kaunar juna da kuma nishadantarwa - saukin kan da marigayi Ras Kimono yake da shi ya sa ya dade akan ganiyarsa.
Da yawa daga mawakan Reggae dai ana alakanta su da shan tabar wiwi, wani abu da ba saban ba.
Marigayi Ras Kimono ya sha nanatawa cewa "Ba na shan taba bana shan wiwi kuma ni ba mai bin mata ba ne."
Daya daga cikin wakokinsa da 'yan Afirka ke matukar kauna ita ce ta "Ayaga yaga yaga yoh".
Yayi zamani da fitattun mawaka kamar Majek Fashek da Shina Peters da Wasiu Ayinde Barrister da Evi Edna Ogholi da dai sauransu.
Ya rasu yana da shekara sittin a duniya.
An haifi Ras Kimono a Asaba cikin jihar Delta a Najeriya, kuma ya mutu ya bar mace daya da 'ya'ya.

0 Comments: