Headlines
Loading...
Arsenal ta gayyaci Kanu don yi wa Wenger ban-kwana

Arsenal ta gayyaci Kanu don yi wa Wenger ban-kwana


Kulob din Arsenal da ke Ingila ya gayyaci tsohon dan kwallonsu kuma dan asalin Najeriya Nwanko Kanu a daya daga cikin bakin da za su kalli wasan karshe da kocin Arsenal Arsene Wenger zai jagoranci kulob din a matsayin wasansa na karshe a filin wasan Emirate a matsayinsa na kocin kulob din.
Wenger dai zai yi murabus ne daga kocin kulob din da zarar an kammala kakar wasa ta bana bayan ya shafe kimanin shekara 22 yana horar da kulob din.
Kanu da sauran bakin da aka gayyata, za su kalli wasan karshe da kocin zai yi a gida ne a jibi Lahadi, da hakan zai kawo karshen horarwar kocin a gida.
Bayanin da kulob din ya fitar a shafin sadarwarsa na twitter ya nuna kulob din ya gayyaci tsofaffin ’yan kwallon kulob din ne da suka yi wasa akalla sau 100 zuwa sama a matsayin bakin da za su halarci filin wasan Emirates a ranar Lahadi mai zuwa.
A shekarar 1999 ce Kanu ya koma Arsenal daga kulob din Inter Milan na Italiya, kuma ya yi wa Arsenal wasa sau 119 inda ya samu nasarar zura kwallaye 37 a raga.  Ya shafe shekara biyar ne a Arsenal kafin ya koma kulob din West Brom.
’Yan kwallon da aka gayyata sun hada da Sol Cambell da Thierry Henry da Tony Adams da Bob Wilson da Frank McLintock da sauransu.

0 Comments: