Headlines
Loading...
'Bom ya tashi da wasu yara a Adamawa'

'Bom ya tashi da wasu yara a Adamawa'


Wani bom da wasu yara guda uku suka tsinta ya tashi da su a garin Mubi da ke cikin jihar Adamawa a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Daya daga cikin yaran ya mutu yayin da biyu suka samu mummunan rauni.
Al'amarin ya faru ne a ranar Lahadi a wani wurin da ake kira Filin Ajakuta inda ake tara karafa zuwa kudancin Najeriya.
Kwamishin watsa labaran jihar Adamawa Ahmad Sajo wanda ya tabbatar wa da Duniyar Yau da faruwar lamarin ya ce "ba harin bom ba ne ko harin kunar bakin wake."
"Wasu yara ne guda uku 'yan jari bola suka tsinci bom, sun yi tsammanin wani abu ne mai daraja da za su iya sayarwa su samu kudi." in ji shi.
Ya kara da cewa bom din ya fashe ne a lokacin da yaran suke kokarin sayarwa ga masu sayen kayan bola.
Ya ce mummunan raunin da yara biyu suka ji, ana tunanin sai an yanke wa dayansu kafa.
Jihar Adamawa na daya daga cikin jihohin arewa maso gabashin Najeriya da suka yi fama da rikicin Boko Haram.
Ana tunanin yaran sun tsinto abubuwan da aka ajiye, ba su fashe ba a rikicin Boko Haram.
Sajo ya ce zai iya kasancewa lokacin da ake gwagwarmaya da Boko Haram, mayakan suka bar shi har yaran suka tsinta suna tsammanin wani abu mai daraja ne su sayar don su samu kudi.
Ya ce an taba samun irin haka a garin Garkida inda wasu yara suka dauko bom daga daji suka kawo gida kuma ya fashe ya yi barna.
Yanzu haka dai ya ce jami'an tsaro na bin diddigin lamarin domin gano inda yaran suka tsinci bom din.
"Binciken jami'an tsaro ya tabbatar da cewa ba an yi amfani da yaran ba ne domin kai hari, illa yaran sun yi baban bola ne da nufin samun kudi" a cewar kwamishinan na watsa labarai.

0 Comments: