A jibi Lahadi idan Allah Ya kai mu za a yi wasa mafi zafi a gasar La-Liga ta Sifen inda kungiyar kwallon kafa ta FC Barcelona za ta kece-raini da kungiyar Real Madrid.
Wasan zai gudana ne da misalin karfe takwas saura kwata na dare agogon Najeriya a filin wasan Barcelona da ake kira Camp Nou.
Kodayake tuni kulob din Barcelona ya lashe kofin La-Liga na bana a makon jiya, amma ana ganin duk da haka wasan zai yi zafi ganin kungiyoyin biyu za su yi duk mai yiwuwa wajen ganin sun kare martabarsu. A wasa zagayen farko da aka yi a gidan Real Madrid, Barcelona ce ta lallasa Madrid da ci 3-0. Kawo yanzu babu kulob din da ya doke Barcelona a wannan gasa, don haka kulob din zai yi duk mai yiwuwa ya ga ya doke na Madrid don ya ci gaba da kafa tarihi.
Sai dai a bangaren Madrid kulob din zai yi kokarin lallasa Barcelona ne don ya karya lagon Barcelona a kokarin kammala gasar ba tare da an doke ta a bana ba, kuma hakan zai daga martabar Crisitano Ronaldo a kokarin lashe kyautar gwarzon dan kwallon duniya a karo na 6 idan ya samu nasarar lashe kofin zakarun kulob na Turai a karo na uku a jere.
Zaratan ’yan kwallo irin su Lionel Messi da Luis Suarez da Andre Iniesta da Iban Rakitic da Umtiti da sauransu ne ake sa ran za su buga wa kulob din Barcelona yayin da a bangaren Madrid ake sa ran zaratan ’yan kwallo irin su Cristiano Ronaldo da Assensio da Lukas barkuez da Toni Kroos da Luka Modric da Marcelo da sauransu ne za su buga wa kulob din a yayin wasan.
A duk lokacin da kungiyoyin biyu suka hadu don gwabzawa da juna an yi kiyasin kimanin mutum miliyan 500 ne suke kallon wasan kai tsaye da kuma a akwatunan talabijin a fadin duniya. Hasalima masana harkar kwallo sun ce babu wasan da ake kallo in ban da gasar cin kofin duniya kamar wasan Barcelona da na Real Madrid.
Kamar kullum ana sa ran gidajen kallon kafa a Najeriya za su cika makil da masoya kwallon kafa don ganin yadda wasan zai kaya.
Sau 25 kenan kulob din Barcelona ya samu nasarar lashe wannan gasa yayin da Real Madrid ta lashe sau 33 a tasrihi.
0 Comments: