Labaran Yau
Yan Siyasa ne suka kitsa labarin EFCC za ta bincike ni – Wamakko
Shugaban Zauren
Sanatocin Arewacin Najeriya, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, Sanata
mai wakiltar Sakkwato ta Tsakiya a majalisar dattijai ta Najeriya, ya
bayyana cewar wasu ‘yan siyasa da ke adawa da shi ne suka kitsa labarin
wai hukumar EFCC za ta bincike shi kan badakalar biliyan 15 da aka batar
a lokacin mulkinsa, har an ga wasu biliyan daya da rabi a asusun
ajiyarsa na banki.
Ya kara da cewar “Wallahi ban taba
mallakar naira biliyan daya ba a rayuwata ta duniya”. Sanata Aliyu
Magatakarda Wamakko ya bayyana hakan ne a zantawarsa da manema labarai a
makon da ya gabata a gidansa da ke Unguwar Gawon Nama a Sakkwato ya ce
‘ni ba mutum ne mai kudi ba, hakazalika b ana aje kudi’.
Wannan bayanin
ya biyo baya ne a lokacin da Sanata Wamakko yake karin haske ga labarin
karya da wasu jaridun Najeriya suka wallafa akan cewar hukumar EFCC tana
tuhumarsa da satar kudi da shi da tsohon Gwamnan Kano, Rabiu Musa
Kwankwaso.
A cikin labarin da wadannan jaridu
suka wallafa, sun bayyana cewa wannan zargi ya biyo baya ne ta hannun
wasu mutane da suka rubuta koke zuwa ga Hukumar EFCC, inda suke neman a
binciki Sanata Wamakko wanda suke hasashen ya kwashi kudin al’umma da
suka cimma biliyan 15 a lokacin da yake a matsayin Gwamnan Jahar Sokoto.
Sanatan ya kara da cewar “dukkan
abin da wadannan mutane suka bayyana a cikin kokensu da suka rubuta zuwa
ga hukumar EFCC karya ne, magana ce maras tushe, kuma kiren karya ne da
yake tattare da zarge-zarge na karya daga mutane masu yada zancen karya
da jita-jita a cikin al’umma, ba magana ce ta hukumar ba ta wasu mutane
ce dole sai sun karya Wamakko sun manta da Allah dai da ya halicce shi
ke iya karya shi, maganar an ga biliyan 1 da rabi a asusuna ba wani
hankali da zai yarda da ita duk masu hankali sun gane wannan labari ne
aka shirya don cin zarafina.”
Aliyu Wamakko ya ce, dukkan wadannan
abubuwa na zarge zarge suna daga cikin shirye-shirye na makiyansa da
kuma ‘yan siyasa da suka sha faduwa zabe a lokacin gwagwarmayar siyasa
da shi wanda kuma har yau suka zama abun kyama ga al’ummar jahar, haka
ma su ne mutane da suke neman ganin cewa Sanata Wamakko ya daina
numfashi a duniya. Sun sha rubutawa EFCC takardu har an taba rubutawa a
gidan wani dan siyasa wai jami’a mallakar jiha da na gina da gidajen
Mana da Kalambaina ba a yi su ba, aka ga ya yi karya. “Ni ban fadi ba na
kuskure ba, in na aiwatar da lamari a bincike ni cikin adalci da
gaskiya.”
“A mulki na yi iyakar kokarina da
sadaukarwa kan amanar da aka damka min na samar da manyan makarantun
gaba da sakandare biyar da gidaje sama da dubu biyar har da gidajen
Alkalai, kilomita 1,000 na titin kwalta da samar da sana’o’i da matasa
dubu 500, bayan samar da kananan asibitocin mazabu da motocin daukar
marasa lafiya, a lokacin ina gwamna ba na yawo, bani yin sati daya bana
cikin jihata, na ziyarci Amurka da Landan sau daya kuma shi ma gayyata
ce na samu,” a cewar Sanata.
“Wannan bincike da ake magana ya
dace ya kasance bisa ka’ida da gaskiya, kuma hakika ni na tabbatar cewa
ban saci kudin kowa ba. A matsayina gwamnan Sakkwato daga shekarar 2007
zuwa 2015, na gudanar da jagoranci da kwatanta gaskiya a cikinsa, da
kula da amanar da talakawan Sakkwato suka damka min ba tare da yin coge
ba.
“Na kalubalanci mutane da suke yada
wannan karya a jaridu da cewar, su wallafa hakikanin gaskiyar takardun
bayanai na asusun ajiya na na bankuna wanda yake nuna hakan, don a gane
ba sharri da karya ce ba.
0 Comments: