Headlines
Loading...
A kama Duk Barayin Da Suka Farfasa Dakin Ajiyan Abinci A Abuja

A kama Duk Barayin Da Suka Farfasa Dakin Ajiyan Abinci A Abuja

A kama Duk Barayin Da Suka Farfasa Dakin Ajiyan Abinci A Abuja

Ministan Abuja ya umarci jami’an tsaro su kama wadanda suka fasa dakunan ajiyan abinci da kayan masarufi na tallafin Korona a Abuja.


A cikin awa 48, matasa da wasu magidanta sun farfasa dakunan ajiya har guda hudu a Abuja su yi wa dakunan karkaf.


Barayin sun dauke babura, Atamfofi, kayan abinci da sauran su.


Tuni dai an aika da jami’an tsaro domin cafke duk wanda suka samu da hukunta su.


A jihar Kaduna ma gwamnati ta umarci jami’an tsaro su bi gida-gida suna kamo wadanda suka barnata kayan abincin sannan kuma gwamnatin jihar ta gargadi mutane kada su ci wadannan abinci da suka sata domin wasunsu da dama ba na ci bane.

0 Comments: