Labaran Yau
Buhari zai sa hannu kan dokar bai wa matasa damar tsayawa takara
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari
ya tabbatar wa da 'yan kasar cewa zai sanya hannu kan dokar nan ta bai
wa matasa damar tsayawa takara nan da kwanaki kadan masu zuwa.
Ya ce: "Nan da 'yan kwanaki kadan zan sadu da matasa da dama na kasar nan domin sanya hannu kan kudurin dokar da za ta bai wa matasa damar tsayawa takara."
A watan Yulin 2017 ne Majalisar dattawan kasar ta amince da kudirin da zai bai wa matasa damar tsayawa takarar a mukaman shugaban kasa da gwamna da majalisun dattawa da na wakilai.
Kudirin dai ya bai wa matasa masu shekara 35 damar shiga takarar neman shugabancin kasar yayin da ya bai wa matasa masu shekara 30 damar neman gwamna.
Haka zalika, kudurin ya amince 'yan shekara 25 su tsaya takarar zama wakilai a majalisar wakilan kasar.
Ana ganin wannan matsaya ta shugaban kasa a wani gagarumin ci-gaba, kuma wasu matasan kasar sun nuna farin cikinsu kan wannan lamari.
A baya dai mutane da dama sun nuna shakku kan ko shugaban zai amince ya sa hannu kan dokar.
Sauran sakon shugaban kasa
A cikin jawabin nasa, Shugaba Buhari ya tabo batutuwa da dama na irin sauye-sauyen da gwamnatinsa ta kawo cikin shekara uku, da kuma wadanda take burin kawowa nan gaba.Ya yi magana kan yadda cikin shekara uku aka samu 'gagarumar nasara' wajen dakile ayyukan masu tayar da kayar baya na Boko Haram, da ceto da yawa daga 'yan matan Chibok da 'yan matan Dapchi da wasu mutum 16,000 da 'yan kungiyar suka sace, da kuma tabbatar da tsaro a sansanonin 'yan gudun hijra.
Sai dai wasu masu sharhi sun sha fadar cewa har yanzu da sauran rina a kaba dangane da batun magance rikicin Boko Haram, ganin yadda 'yan kungiyar ke ci gaba da kai hare-haren kunar bakin wake.
Rikicin manoma da makiyaya
Shugaba Buhari ya tabo batun yadda ake samun karuwar rikice-rikice tsakanin manoma da makiyaya a jihohin kasar da dama, yana mai cewa al'amarin ba mai dadi ba ne, amma "gwamnati na iya bakin kokarinta don ganin an magance wannan matsala."Ya kuma tabo batun yadda gwamnatinsa ta samu nasara a yaki da cin hanci da rashawa, da samar da ayyukan yi da kuma bunkasa tattalin arziki.
Shugaba Buhari, wanda ya dare mulkin kasar a 2015, ya ayyana aniyarsa ta sake tsayawa takara a 2019.
Sai dai ana yawan sukarsa kan yadda gwamnatinsa ta kasa ciyar da tattalin arzikin kasar gaba, amma a jawabin nasa na ranar Talata, ya ce duk da irin kalubalen da ake fuskanta, a yanzu tattalin arzikin na bunkasa.
0 Comments: