Shugaban kwamitin dattijai a kan babban birnin tarayya Abuja, Sanata Dino Melaye (APC, Kogi), ya ce, bai shirya shiga zauren majalisar dattijan domin ci gaba harkokin majalisa jiya ba. dan majalisar dattijan daga jihar Kogi, ya kara da cewa, har yanzu jikinsa bai yi karfi sosai ba da zai iya ci gaba gudanar da aiyukan majalisar. Sai dai ya ce, masu koarin rufe bakinsa daga Magana a kan mulkin danniya dam aka karya sun yi asara, domin kuwa yana nan daram a kan bakansa.
Zargin safarar makamai da rundunar ‘yansada ke yi wa Melaye ta sarkake har ta kai ga kais hi asibiti inda aka gabatar das hi gaban kotu a kan gadon asibiti. A wani sako daya aikawa Manama labarai ta kafar WhatsApp, ya matukar nuna godiyarsa ga daukacin ‘yan Nijeriya, ya ce, zai ci gaba da bayyana gaskiya ba tare da tsoro ba. Sakon ya ci gaba da cewa,
“A ‘yan makwannin nan an yi kokarin danne ni daga fadin gaskiya, amma kasanwar ku a baya na a wannan lokaci mai mahimmanci, a halin yanzu na dawo da karfi na, ba za a iya rufe baki na ba daga fada da mulkin danniya da siyasar danniya da cin zarafin mutane. “Sun dandana mani wahala kala kala amma da karfin Allah da kuma goyon bayanku ‘yan Nijeriya mun samu nasara, gaskiya tayi nasara a kan karya da ma karyata.
“Gwamnati dirra mani da dukkan karfinta ta turo mani ‘yansanda 200 da muggan makamai, sun yi haka ne saboda na kira rashin adalci da sunasa na kuma yi kira da ayi aiki a bayyane tare da bin dokokin aiki, a saboda haka ne suke son su nakasa ni gaba daya” inji shi. A kan kokarin da aka yin a yi masa kiranyen da aba a samu nasara ba, “A lokacin da nake cikin duhu bani kuma da karfin fada ko kwato wa kai na ‘yanci, sun nemi kwace iko da matsayi na, wanda kuka bani da kanku ba tare da wani takurawa ba, amma fitowarku ya dakushe wannan mummunar hankorosu, amma amsawarku ya tsayar da wannan mumumunan shirin nasu, kun yi tsayin daka na kare matsayin da kuka bani, ina mautukar godiya a gareku da dukkan zuciyata, a kokarin su na karya ni sun kara mani karfi ne kawai” inji shi.
0 Comments: