Kama yanzu jihohi guda goma ne tare da babban tarayya akayi warwason abinci a ciki. Jihohin da lamarin ya auku sun hada da:
Kaduna
A jihar Kaduna an samu rahoton cewa wasu matasa sun kunna kai wani gidan ajiyar abinci da ke Barnawa, tare da kwashe kayan abincin da aka ajiye.
Sai dai gwamnatin jihar ta ce wasu daga cikin kayan da aka kwashe an ɗebe su ne a wani wuri da hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasa NAFDAC ke ajiye abincin da ya lalace.
Taraba
A ranar Asabar 24 ga watan Satumba ne dandazon jama'a suka yi wa wani gidan ajiyar kayan abinci da ke birnin Jalingo ƙawanya duk da jami'an tsaron da ke gadinsa, tare da kwashe dukkanin kayan abincin da aka ajiye.
Wannan al'amari ya sa gwamnatin jihar ta ɗauki matakin sanya dokar hana fita ta tsawon sa'a 36 domin daƙile lamarin.
Adamawa
A jihar Adamawa, gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita ta tsawon awa 24, bayan samun wasu matasa da kwashe kayan da aka ajiye don tallafa wa waɗanda annobar korona ta janyowa shiga garari.
Gwamnan jihar Ahmadu Umaru Fintiri ya ce an riga an raba kashi hudu na kayan, kashi daya ne kawai ya rage ba a bai wa jama'a ba, kuma su ma ɗin za a bayar da su ne ranar Litinin ɗin nan.
Filato
Mutane sun shiga wani gidan ajiyar abinci da ke Buruku, a Jos Ta Kudu.
Sai dai gwamnatin jihar ta fitar da wata sanarwa, in da ta ce ba ta ɓoye komai ba, hasalima ta gama raba waɗanda ta karɓa daga ma'aikatar jin ƙai tun a ranar 16 ga watan Octoba.
Bauchi
Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya ce wasu mutane sun yi yunƙurin shiga wani gidan ajiyar abinci na gwamnatin jihar da zummar kwashe kayayyakin da ake ciki, amma ba u tarar da komai ba, domin tuni gwamnati ta raba su ga mutane.
Legas
A jihar Legas ranar Alhamis ne wasu matasa suka kwashe kayan abinci a inda aka ajiye su a unguwar Maza-Maza, tare da kwashe komai a ciki.
Hakan na zuwa ne bayan da rikici ya ɓarke a jihar sakamakon zanga-zangar End SARS wadda ta rikiɗe ta zama rikici.
Ekiti
A nan ma an kwashe kayan abinci a inda ake ajiye da su a birnin Ado Ekiti, amma gwamnatin jihar ta ce suna ɗauke da sinadarai.
Sanarwar gwamnatin jihar ta ce an kwashe abincin ne a wani wuri da hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar wato SEMA ke ajiye taki, amma sai mutane suka yi zaton garin kwaki ne.
Kogi
Mutane sun fasa wani gidan ajiyar abinci da ke birnin Lokoja, amma gwamnatin jihar ta ce tuni ta raba tallafin na cutar korona.
Sanarwar da gwamnatin jihar ta fitar ta gode wa mutanen, bisa yadda suka je suka debi nasu kason.
Osun
Mutane sun shiga gidan Cocoa da aka jibge tarin kayan abinci tare da kwashe su.
A cewar gwamnatin jihar, kayan na hannun kwamitin raba kayan tallafi na fadar shugaban kasa har yanzu, don haka ba su zama nata ba tukunna.
Abuja
A babbar tarayya abuja an samu rahoton cewa wasu tsageru matasa sun fasa gidan ajiyar abinci guda hudu, tare da kwashe kayan abincin, babura, Atamfofi da sauransu da aka ajiye.
0 Comments: