Headlines
Loading...
Yadda rijiyoyi ke cinye rayukan jama'a a Kano

Yadda rijiyoyi ke cinye rayukan jama'a a Kano

Akalla rayukan mutum 20 ne wadansu rijiyoyi suka ci a unguwanni daban-daban a jihar Kano, kamar yadda hukumar kwana-kwana ta jihar ta bayyana wa BBC.

Hukumar ta ce adadin ya kai 34 idan aka hada da mutanen da ruwa ya ci a koguna tsakanin watan Janairun bana zuwa yanzu.

Zulaiha Bashir, wadda ba ta wuce shekara takwas ba a duniya, tana daya daga cikin mutanen da wata rijiya ta yi ajalinsu a watan Afrilu lokacin da ta je neman ruwan wanka a unguwar Hotoro.

Mahaifiyar marigayiyar Haddaniya Bashir ta shaida wa wakilin BBC Pidgin Mansur Abubakar a Kano cewa: "Abin da ya faru da diyata abu ne da ba zan mantawa da shi ba har karshen rayuwata."
"Ina zaune tare da Zulaiha a kusa da wata bishiya a gidanmu. Sai kawai ta ce min tana jin zafi. Ni kuma sai na ba ta shawarar ta ta je ta nemi ruwa ta yi wanka."

Haddaniya ta ci gaba da cewa: "Bayan ta jawo gugar farko ce, tana kan jawo ta biyu ne sai kawai ta zame ta fada cikin rijiyar. Sai kuma aka yi rashin sa'a, babu wani a kusa da zai taimaka maka. Wannan ce ranar bakin ciki da ba zan taba mantawa da ita ba a rayuwata."

Ta ce duk da cewa "mu Musulmi mun yarda da kaddara. Amma da a ce muna da ruwan fanfo a gidan nan ko kuma kusa da gidan da watakila wannan abin bakin cikin bai faru da mu ba."


"A baya gwamnati tana kawo mana motar ruwa don amfaninmu, amma yanzu an daina kawowa," in ji ta. Har ila yau, ta bukaci gwamnati da ta yi wani abu game da killace rijiyoyin da kuma yi musu murafe. Kodayake, mahaifin marigayiyar Malam Bashir Hotoro ya ce shi ba zai iyana magana ba, saboda bakin cikin da yake ciki na rashin diyarsa.

Amma shi ma wani mahaifi wanda karamin dansa Farook Aminu, mai shekara uku, ya mutu a wata rijiya ya bukaci hukumomi da su dauki matakai don tabbatar da ana bin ka'idoji wajen gina rijiyoyi.
Sai dai mai magana da yawun gwamnan jihar Kano Aminu Yassar ya ce batun ba shi da nasaba da karancin ruwan da ake fuskanta a jihar.

"Duk wanda ya san tarihin Kano da sauran jihohin arewacin Najeriya, ya san cewa rijiya tana daya daga cikin muhimman abubuwan da muke rayuwa da su."
"Maganar nan da muke, na gina rijiya a gidana ko mako daya ba a kai ba," in ji kakakin gwamnatin jihar. Hakazalika ya ce "magana ce kawai ta kula da ka'idojin gina rijiyoyi don kaucewa hadari, kamar yadda 'yan kwana-kwana suke bayani."


Jami'in hulda da jama'a na hukumar kwana-kwana ta jihar Kano Saidu Ibrahim ya ce mafita ga wannan matsalar shi ne "ilmantar da jama'a game da yadda za su kiyaye amfani da rijiyoyi ba tare da jefa rayukansu cikin hadari ba. "

A karshe ya ce sabanin yadda yawancin mutane suke tunani, "ba kananan yara ne kawai suke shiga hadarin fada wa cikin rijiya ba." "A'a, manya ma abin yana rutsa wa da su kuma hakan ya sa muke ganin akwai bukatar a rika wayar wa jama'a kai game da hadarin da ke tattare da rijiya," in ji shi.

0 Comments: