Headlines
Loading...
Annoba A Kaduna: An Sace Mutum 42 A Birnin Gwari

Annoba A Kaduna: An Sace Mutum 42 A Birnin GwariA wani farmaki da ‘yan ta’adda suka kai a kan hanyar Birnin-Gwari zuwa Kaduna sun sace fasinjojin 42 dake a kan hanyarsu zuwa Kano a cikin awa 24. 

Wani shugaban kungiyar motoci ta NURTW, a Birnin-Gwari ya bayyana wa ‘yan jarida cewa, lamarin ya faru ne da yammacin Talata zuwa safiyar Laraba. Shugaban kungiyar daya bukaci a sakaya sunansa ya kara bayyana cewa, “A kalla fasinjoji 42 ne aka sace a kan hanyar Birnin-Gwari zuwa Kaduna a tsakanin yammacin jiya zuwa wannan safiyar. 

“A wannan Larabar da misalin karfe 8.00 na safe, wasu ‘yan ta’adda sun kama motoci uku dake dauke mutane 21 daga garin Birnin-Gwari zuwa Kuriga zuwa Kagara inda suka yi garkuwa a dajin Allah. “Haka kuma, jiya da yamma misalign karfe 5:15 na asuba, aka sace wasu mutane 21 a cikin mota kirar BW Golf (saloon). “Wasu daga cikin direbobin da suka arce bayan sun hango ‘yan ta’addan ne suka yi mana bayanin abin daya faru dasu.

 “Ya wancin fasinjojin mata da yara kanana ne dake a kan hanyarsu zuwa Kano a lokacin da aka sace su” inji shi. Bayanai sun  nuna cewar, an riga an sanar da hukumomin tsaron daya kamata, suna nan kuma sun fara shirin cetosu tare da hukunta masu garkuwa da mutanen. zRecall that PRNigeria had reported actibities of armed bandits operating along Birnin-Gwari-Kaduna Highways where they  a iya tunawa, a ‘yan kwanankin nan an sace fasinjoji 107, abin daya sanya shugaban rundunar sojojin Nijeriya, 

Tukur Buratai ya hori sojoji dasu kawo karshen barnatar da kashe kashen rayuka da barnatar da dukiyan jama’a da ake yi a yankin a cikin makonnin uku. A kan haka ne kungiyar direbobi ta NURTW ta sanar da ‘yan kungiyar dasu guji bin hanyar har sai an samar da cikakken tsaro a kan hanyar. Wani jami’in kungiyar NURTW ya ce, yawanin wadanda aka sace suna tafiya ne tsakanin Arewaci zuwa Kudancin kasar nan.


0 Comments: