Ana Zargin Jami'an Tsaro Da Yan Siyasa Wajen Taimakawa Ga Kwashe Kayan Al'umma A Jihar Adamawa
Duk Da Dokar Hana Fita na tsawon awanni ashirin da hudu, Gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya yi zargin cewa wata babbar makarkashiya da wasu ‘yan siyasa masu karfi ke yi na ruguza jihar ta hanyar barin ci gaba da sace-sace.
Fintiri wanda ya yi magana ta bakin Babban Daraktansa na Watsa Labarai da Sadarwa, Solomon Kumangar, ya caccaki hukumomin tsaro saboda rashin son aiwatar da dokar hana fita da aka sanar a ranar Lahadi.
Ya lura cewa wasu daga cikin shugabannin tsaro a jihar sun bijire wa batun kafa dokar hana fita kwanaki kadan da suka gabata don hana halin da ake ciki yanzu kuma daga karshe da aka fara satar a ranar Lahadi, sai jami'an tsaro suka ki daukar mataki.
Ya bayar da hujjar cewa lokacin da aka sanar da dokar hana fita a wasu jihohin da suka hada da Lagos, Filato, Kaduna Delta da Taraba, sai hukumomin tsaro suka hanzarta shiga don aiwatar da doka, suna mamakin dalilin da ya sa aka kyale miyagu ke wawashe cikin 'yanci a cikin dokar hana fita a jihar.
0 Comments: