Shugaban zai tsawaita shekara 18 da ya shafe yana mulkin kasar, wanda magoya bayansa ke cewa ya farfado da martabar kasar a duniya, yayin da 'yan hamayya ke bayyana mulkinsa da ta kama karya kamar yadda BBC ta ruwaito.
A ranar Asabar da ta gabata, aka samu yamutsi tsakanin masu zanga-zangar adawa da salon mulkin shugaban da jami'an tsaro
Sama da mutum dubu daya aka cafke a biranen kasar 19 lokacin zanga-zangar.
Putin zai karbi rantsuwar kama aiki ne a dandalin da aka nada tsofaffin sarakunan Rasha, a kasar da ta fi kowacce fadin kasa a duniya, kuma za a takaita shagulgula.
Rahotanni sun ce wadanda suka ba da gudunmawa a lokacin yakin neman zaben Mista Putin, mai shekaru 65, ne kawai za su halarci bikin rantsar da shi.
Mista Putin na fuskantar manyan kalubale da kuma takukuman karayar tattalin arziki da tasirinsu ke bayyane.
0 Comments: