Headlines
Loading...
Mata A Nigeria Sun Bukaci A Basu Mukamin Mataimakin Shugaban Kasa A Shekara Ta 2019

Mata A Nigeria Sun Bukaci A Basu Mukamin Mataimakin Shugaban Kasa A Shekara Ta 2019


Mata yan majalisar dokoki a tarayyar Nigeria sun bukaci a basu makamin mataimakin shugaban kasa bayan zaben shekara mai zuwa ta 2019.
Kungiyar mata yan majalisar dokoki a tarayyar Nigeria, wato "The Conference of Nigerian Female Parliamentarians (CONFEPA)" ce bukaci hakan a wata ganawar da suka yi tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya Jumma'a. Shugaban kungiyar Malama Elizabeth Atevie ta kara da cewa tsarin siyasar Nigeria ya maida mata saniyar ware a kasar.
Elizabeth ta kara da cewa a halin yanzu an gudanar da zabubbuka har sau 5 a kasar tun shekara ta 1999, amma maza sun mamaye mafi yawan mukaman siyasa na kasar a cikin wannan lokaci.
Shugaban kungiyar ta CONFEPA ta kara da cewa a halin yan mace guda kacal take rike da mukami a majalisar dattawan kasar, sannan matan kasar 8 ne kacal suka zama sanatoci a majalisar dattawan kasar mai sanatoci 109, a yayinda mata 22 kacal suke cikin majalisar wakilan kasar mai wakilai 360.
Wannan shi ne kashe 5% a majalisun dokokin kasar. inji Malama Elizabeth. Daga karshe.

0 Comments: