Headlines
Loading...
Masu fafutikar ba mata damar tuki a Saudiyya na fuskantar barazana

Masu fafutikar ba mata damar tuki a Saudiyya na fuskantar barazana

Jagorar gangamin da ya rika neman a bai wa mata damar tuki a Saudiyya ta ce ita da sauran masu fafutika da ke kasar na fuskantar barazanar kisa.

Manal al-Sharif ta ce an rika turo mata da sakwannin i-mail inda aka yi mata barazanar kisa kafin a janye a haramcin tukin motar.

Ta bayyanna haka ne bayan da aka kama wasu mata masu fafutika a kasar. Ana tuhumarsu da cin amanar kasa da kuma aiki tare da gwamnatocin yamma -zargi ne da kungiyar kare hakin bil'adama ta Amnesty International ta kira "dabarun saka tsoro." "Ana zargin mambobin kungiyar da tuntubar wasu cibiyoyin kasashen waje domin kawo nakasu ga tsarin zaman lafiyar kasar," in ji kungiyar Amnesty .
Manal al-Sharif, wadda a halin yanzu ta na zaune a kasar Australiya ta ce kamfe din "shafa kashin kaji da aka kitsa" wa masu fafutikar ya yi kama da irin na shekarar 2011. A ranar 24 ga watan Yuli ne za a janye dokar.

'Ana kai wa masu bayyana ra'ayi samame'

Mutane bakwai ne aka kama da suka hada da maza da mata a baya-baya nan ciki har da Loujain al-Hathloul, wata mai rajin kare hakkin mata masu tuki. A baya an taba tsare Madam Hathloul lokacin da ta yi kokarin tuka mota zuwa kan iyakar kasar da Hadaddiyar Daular Larabawa.Ta shafe kwanaki 73 tana tsare a cibiyar gyara halinka, kuma ta rika bayyana ra'yoyinta a shafin Twitter.


Masu fafutikar ba mata damar tuki a Saudiyya na fuskantar barazana

Kungiyar Amnesty ta yi amannar cewa an kama Eman al-Nafjan da Aziz al-Yousef, da Dr Aisha al-Manea, da Dr Ibrahim al-Modeimigh, da Mohammad al-Rabea wadanda dukaninsu masu rajin kare hakin mata ne.

Dokokin Saudiyya sun bukaci mata su rika neman izinin maza kan wasu shawarwari ko mataki, kuma hana mata tuki na daya daga cikinsu. A baya wannan na nufin cewa sai iyali sun dauki hayar direban da zai rika fita da 'yanuwansu mata.

Yarima mai jiran gado Mohammad Bin Salman, ya aiwatar da sauye-sauye da dama a cikin kasar mai tsattsauran ra'ayin addinin musulunci.

Sai dai Amnesty Internatiol ba ta soke shi da komai ba a cikin sanarwar da ta fitar."Yarima mai jiran gado Mohammad Bin Salman ya bayyana kansa a matsayin mai "kawo sauyi", Sai dai babu wani abin a zo gani game da wannan alkawari, ganin yadda ake kara kaimi a samamen da ake kai wa masu bayyana ra'ayoyinsu a masauratar," in ji Amnesty.

"Alkawarin da ya yi bai yi tasiri ba saboda ana tsare da wadanda suka rika fafutika cikin lumuna wajan ganin an bai wa mata damar zuwa wurin da suke so, kuma a daidaita tsakaninsu da maza."0 Comments: