Headlines
Loading...
An kashe akalla mutum 45 a Birnin Gwari

An kashe akalla mutum 45 a Birnin Gwari

Akalla mutum 45 ne suka rasa rayukansu a harin da ‘yan bindiga suka kai kauyen Gwaska a karamar hukumar Gwari da ke Jihar Kaduna.
Kwanishinan ‘yan sandan Jihar Kaduna Austin Iwar ya shaida wa kafar Reuters cewa, “Ranar Asabar mun dauko gawawwaki guda 12, sannan kuma a ranar Lahadi muka samu guda 33.”
Wani wanda ya tallafa wajen kwashe gawawwakin da aka samu ya shaida wa Aminiya cewa ‘yan bindigan wadanda ake zargi daga Jihar Zamfara suka zo, sun kuna gidajen mutane, wanda hakan ya sa mutane wadanda yawanci mata ne suka arce zuwa gundumar Doka domin samun mafaka.
“Sun yi kusan awa uku suna yin wannan ta’addanci. Yawancin wadanda suka samu rauni kuma an kai su asibitin Birnin Gwari.
“Lokacin da muke isa garin, mu tadda wasu gidajen suna cin wuta, sannan muka ga wata mota kirar Hilux dauke da gawawwakin mutane.”
Sannan ya kara da cewa za a iya gano wasu gawawwakin daga baya.
Jadawalin yadda aka kashe mutane da da a cikin 'yan kwanaki kadan a Birnin Gwari

0 Comments: