Hukumar zaben Najeriya, ta ce yakamata al'ummar kasar su kwantar da hankulansu a kan batun zaben 2019 da ke karatowa.
Malam Aliyu, ya ce a zaben 2019, ba wanda zai kai ga nasara sai wanda jama'a ta zaba, sai kuma wanda goyon bayansa ya bayyana wato wanda kuri'a ta zaba.
Mai magana da yawun hukumar zaben ya ce, ' Tanadin hukumar zabe a kullum shi ne a tabbatar da sahihin zabe a 2019'.
Malam Aliyu Bello, daga cikin matakan tabbatar da sahihin zabe a 2019, shi ne tuni aka fara bayar da rijistar zabe ga wadanda suka basu da ita, ko kuma wadanda suke da ta wucin gadi.
Game da batun zargin da wasu 'yan kasar ke yi kan cewa hukumar na shirin kirkirar haramtattun rumfunan zabe har 30,000 da nufin tafka magudi a zaben 2019, Malam Aliyu ya ce, gaskiyar lamari ba bu wannan magana, hasali ma shugaban hukumar zaben ya tabbatar da cewa, daga yanzu har zuwa lokacin zaben, ba bu wani kuduri a hukumar na kirkirar rumfunan zabe har 30,000.
Mai magana da yawun hukumar zaben ya ce, hukumarsu ba ta yin abu a cikin rufa-rufa, idan har hukumar zata yi wani abu, to ta kan fitar da dalilai da bayanai, sannan kuma ta bi matakai na abinda doka ta aminta da su.
Tuni dai hankulan jama'a a Najeriyar ya fara karkata a kan zaben na 2019.
Baya ga matasa wadanda ke da burin ganin an sa hannu a dokar da za ta rage shekarun tsayawa takara, wasu kuma tsokaci suka fara yi a kan shirye-shiryen gudanar da sahihin zabe.
Bayani kan zaben 2019
Tuni dai hukumar zaben Najeriya ta fitar da jadawali zaben 2019, inda za a fara da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar tarayya.Sai kuma zaben gwamnoni da na 'yan majalisun jiha. Hukumar zaben ta kuma tabbatar da cewa za a yi sahihin zabe wanda ba bu magudi a cikinsa.
0 Comments: