Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana Alhamis A Matsayin Ranar Hutu Na Maulidi
Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranar Alhamis, 29 ga watan Oktoban 2020 a matsayin ranar hutu domin bikin ranar haihuwar annabi Muhammad (S.A.W).
Ranar dai ita ce ta zo daidai da 12 ga watan Rabi’ul Auwal, wata na uku a kalandar Musulunci kuma ranar da ta dace da ta haihuwar ma’aikin.
Ministan Cikin Gida, Rauf Aregbesola ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a madadin gwamnatin ta bakin kakakin ma’aikatarsa, Mohammed Manga a ranar Talata.Sanarwar ta taya daukacin al’ummar Musulmin Najeriya murnanar zagayowar ranar tare da yin kira gare su wajen koyi da halin ma’aikin musamman wajen kaunar juna, hakuri da kuma son zaman lafiya.
Ministan ya kuma yi kira ga ‘yan Najeriya musamman Musulmai wajen ganin sun kauracewa rikici, karya doka da kuma tayar da zaune tsaye, yana mai cewa kamata ya yi Najeriya a matsayinta na kusa a nahiyar Afirka ta zama abar kwatance a tsakanin kasashe takwarorinta.
Ya kuma ja kunnen su kan su guji yin duk wani abinda zai raba kan al’umma, su kuma taimakawa aniyar shugaba Buhari ta ganin an gina kasa abar alfahari ga kowa.
Musulmai dai a fadin duniya kan yi shagulgulan ranar kasancewar ita ce aka haifi annabi Muhammad (S.A.W) sama da shekaru 1400 da suka shude a birnin Makkah na kasar Saudiyya.
0 Comments: