'Yan sanda sun yi harbi sama domin
tarwatsa magoya bayan tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau lokacin da aka
gurfanar da shi a gaban kotu a Kano.
An baza 'yan sanda a gaban kotun da aka gurfanar da Malam Ibrahim Shekarau
'Yan sanda sun yi harbi a sama da harba hayaki mai sa hawaye lokacin da aka fito da Shekarau bayan gama zaman kotun
Wakilin BBC yana cikin wadanda suka sha hayaki mai sa hawaye
Hukumar EFCC ce ta gurfanar da tsohon gwamnan kan zargin hatta kudin haram
Duka mutanen uku sun musanta zargin da ake musu, kuma a yanzu an bayar da belinsu
0 Comments: