Mataimakin
Shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya bayyana cewa Shugaba Muhammadu Buhari ne
ya zabe shi mataimakinsa bayan ya yi shawara da Jam’iyyar APC inda suka
yi takara tare kuma suka ci zabe a shekarar 2015.
Osinbajo wanda ya bayyana haka
lokacin da yake amsa tambayoyin da daliban makarantar Life Camp suka yi
masa yayin bikin ranar littafi ta duniya a makon da muke ciki.
“Bayan da
shugaban kasa ya gana da jam’iyarmu sai ya yanke shawarar nada ni wanda
zai zama mataimakinsa inda muka tsaya takara tare muka tsaya zabe kuma
muka yi nasara a zaben shekarar 2015,” in ji shi.
Ya bayyana cewa kafin lamarin yana
koyar da aikin lauya ne a jami’ar Awolowo da ke Jihar Legas. Da yake
amsa tambaya kan samar da kayayyakin more rayuwa a Najeriya, sai ya ce
samar da kayan more rayuwa hakki ne na gwamnati tare da hadin gwiwar
kamfanoni masu zaman kansu.
Ya kara da cewa gwamnati ita take da
alhakin samar da hanyoyi da asibitoci da makarantu da sauran kayan more
rayuwa. Ya bayyana cewa gwamnati na karawa kamfanoni kwarin gwiwa don
su ma su tallafa wajen samar da kayan more rayuwa ga al’ummar kasa baki
daya.
Da aka tambeye shi ko yana da
sha’awar zama shugaban kasa sai ya ce “Ni yanzu matsayina na mataimakin
shugaban kasa ne”. Daga nan sai ya bayyana cewa lamarin mulki abu ne mai
mutukar wahalar gaske saboda nauyin da ke tattare da shi.
0 Comments: