Headlines
Loading...
Karo na biyu AC Milan ta yi rashin nasara a Serie A ta bana

Karo na biyu AC Milan ta yi rashin nasara a Serie A ta bana

Karo na biyu AC Milan ta yi rashin nasara a Serie A ta bana

 AC Milan ta yi rashin nasara a gasar Serie A da ta buga a gida da Atalanta ranar Asabar.

Atalanta ta yi nasara da ci 3-0 a fafatawar da suka yi a San Siro, kuma an rage tazarar maki biyu tsakanin Milan ta daya da Inter ta biyu a teburi.

Cristian Romero ne ya fara cin kwallo, sannan Josip Ilicic ya kara na biyu a bugun fenariti, sai Duvan Zapata da ya kara na uku.

A gefe guda kuma Inter Milan ta barar da damar hadi maki iri daya da Milan, bayan da ta tashi ba ci a karawar da ta yi a gidan Udinese.

Wannan ne wasa na biyu a kakar bana da aka doke Milan a Serie A, bayan 3-1 da ta yi rashin nasara a hannun Juventus ranar 6 ga watan Janairu.

Milan wadda ta yi wasa 19 a gasar Serie A ta ci wasa 13 da canjaras hudu da rashin nasara a fafatawa biyu.

Kungiyar ta ci kwallo 39 an kuma zura mata 22 a raga, mai maki 43.

Atalanta wadda ta doke Milan ranar Asabar ta yi sama zuwa mataki na hudu a teburin Serie A da maki 36.

Wasa biyar da Milan za ta buga nan gaba:

Ranar Talata 26 ga watan Janairu Coppa Italiya

Inter da Milan

Ranar Asabar 30 ga watan Janairu Serie A

Bologna da Milan

Ranar Juma'a 5 ga watan Fabrairu Serie A

Milan da Crotone

Ranar 13 ga watan Fabrairu Serie A

Spezia da Milan

Alhamis 18 ga watan Fabrairu Europa League

Red Star Belgrade da Milan

0 Comments: