Headlines
Loading...
Kashe-kashen da ake a Najeriya ba su taka kara sun karya ba – el-Rufa'i

Kashe-kashen da ake a Najeriya ba su taka kara sun karya ba – el-Rufa'i



Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir el-Rufa'i ya ce manema labarai ne kawai ke zuzuta kashe-kashen da ake yi a kasar, yana mai cewa ba su taka kara sun karya ba.

A hirarsa da BBC, gwamnan, wanda aka kashe akalla mutum 50 a mako guda a jiharsa, ya ce "wani lokaci 'yan jaridu ne suke daga abin... ya zama babba, har ma ya bata wa kasar suna."
"Najeriya babbar kasa ce, babu yadda za a yi a ce rashin tsaro a wani kauye ko wani gefe na kasa ya sa a ce duk kasar babu tsaro," in ji gwamnan, wanda na hannun damar Shugaba Muhammadu Buhari ne.
Ba ya ga rikicin Boko Haram a arewa maso gabashin kasar, ana fama da rikici tsakanin makiyaya da manoma, da sace-sacen mutane domin neman kudin fansa da kuma rikice-rikicen kabilanci da na addini a kasar.
Wasu masu sharhi da dama na ganin gazawar gwamnati wurin dakile wadannan rikice-rikice, sai dai ta dage cewa tana yin iya kokarinta.
Jihar Kaduna na cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da matsalar barayin shanu da 'yan fashi da yawaitar sace-sacen mutane domin neman kudin fansa.
Amma Gwamna Nasir el-Rufa'i, wanda ke magana a wurin wani taron zuba jari a Abuja, ya ce bai kamata a ce duk Najeriya babu tsaro ba saboda ana fama da matsalar tsaro a wata jiha
A cikin mako daya an sace mutum fiye da 130 a jihar Kaduna kawai, ban da mutanen da aka kashe a jihar da sauran sassan kasar.

'Kama da Boko Haram'

Matsalar barayin shanu da satar mutane yanzu ta fi kamari a yankin Birnin Gwari da ke makwabtaka da jihar Zamfara.
Sai dai kuma el-Rufa'i ya ce rikicin barayin shanu da masu satar mutane, matsala ce da ta yi kama da rikicin Boko Haram, saboda yadda suke kashe mutane su kona gari.
"Ya kamata a dauke su kamar Boko Haram, gwamnatin tarayya ta sa sojojinta na sama da kasa su yi maganinsu," in ji gwamnan.
Ya ce gwamnatinsa ta yi kokarin magance rikicin kabilanci da aka dade ana yi a kudancin jihar.
Ya kuma ce duk da matsaloli na tsaro da jihar Kaduna ke fama da su an zuba jarin fiye da dala miliyan 500 a cikin shekara biyu zuwa uku a jiharsa.

0 Comments: