Labaran Yau
Abin da ya sa za mu lashe zabukan kananan hukumomin Kaduna – Shugaban APC
Shugaban
Jam’iyyar APC a karamar Hukumar Jama’a da ke Jihar Kaduna, Alhaji
Ibrahim Aliyu Koli ya ce a shirye jam’iyyarsu take don tunkarar zaben
shugabannin kananan hukumomin Jihar Kaduna da ke tafe don lashe kananan
hukumomin jihar gaba daya.
Shugaban ya bayyana haka ne a
lokacin da yake amsa tambayoyin Aminiya a ofishin jam’iyyar da ke
Kafanchan. Ibrahim Koli, ya kara da bayyana cewa aikace-aikacen da
gwamnan jihar yake shimfidawa a ko ina a fadin jihar Kaduna da suka hada
da gyaran kananan asibitoci da makarantun firamare da shimfida hanyoyi
da inganta harkokin tafiyar da mulki sun isa zama shaida kan dalilin
lashe zabukan da ke tafe.
“Duk surutan da
‘yan adawa za su yi sai dai su yi na son zuciya amma dai kowa ya san
idan rana ta fito babu wani tafin hannu da zai iya kare ta daga
haskakawa,” in ji shi.
Da ya waiwaya kan matsalolin cikin
gida na APC, ganin yadda wata ‘yar takara a karamar hukumar Jama’a ta
buga fostocinta tana yadawa a matsayin halastacciyar ‘yar takarar
shugabancin jam’iyyar domin raba hankulan jama’a, alhali akwai Kwamred
Cecelia Musa wacce ita ce halastacciyar ‘yar takarar jam’iyyar a karamar
hukumar, inda ya ce masu yin haka a kowace karamar hukuma suna batawa
kan su lokaci ne domin hukumar zabe ta jiha ta san wanene ba wanene ba.
0 Comments: