Headlines
Loading...
Sanata Marafa Ya Tallafa Wa  ’Yan Gudun Hijira A Zamfara

Sanata Marafa Ya Tallafa Wa ’Yan Gudun Hijira A Zamfara




A jiya ne Sanata mai wakiltar yankin Zamfara ta tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Kabiru Garba Marafa ya bayar da tallafi ga dimbin al’ummar da suke gudun hijira a garin Mada ta Jihar Zamfara.

Wannan tallafi da Sanata Marafa ya bayar da wannan tallafi ne domin tausaya al’ummar da suka tsinci kawunansu a cikin wannan mawuyacin hali na yin gudun hijira bayan ‘yan bindiga sun tarwatsa su a mabambantan garuruwansu dake sassan Jihar Zamfara.

Yayin gabatar da sakon tallafin, wakilin Sanata Marafa ya bayyanawa Sarkin Mada, da dandazon ‘yan gudun hijiran cewa, Sanata Marafa na cikin matukar damuwa dangane da halin da ‘yan gudun hijiran suke ciki. Wakilin nasa ya bayyana cewa, wannan sakon a matsayin somin tabi ne, kuma tallafin gaggawa domin a taimakawa ‘yan gudun hijiran da abin da za su ci. 

Sanata Marafa ya bayyana cewa, zai yi tattaki da kansa domin ya zo ya ziyarce su don ganin halin da suke ciki daga baya. Daga cikin dimbin kayan tallafin da Sanatan ya aikawa ‘yan gudun hijiran sun hada da buhunan Shinkafa, katon-katon din taliya, Man ja, Man gyada da sauransu.

A jawabinsa, Sarkin Mada ya bayyana godiyarsa ga Allah bisa samuwar Sanata Marafa a Jihar Zamfara. ya ce; “Muna godiya ga Allah (T) da ya halitto mana wannan bawan Allah a cikin Zamfara, shi ne Sanata Kabiru Marafa. Wannan jajircewa da yake yi da irin wannan tallafi da yake bayarwa, wannan ba shi bane karo na farko. ba sai a yankinsa kawai yake kai tallafi ba, a duk fadin jihar yake kai wa. Mun san yana iya kokarinsa. Duk wata ya kan aiko da tallafi nan. Muna godiya a madadin uwayen kasa na wannan yankin.”


0 Comments: