Headlines
Loading...
Zakarun Turai: Magoya bayan Liverpool na cikin tsaka mai wuya

Zakarun Turai: Magoya bayan Liverpool na cikin tsaka mai wuya

Daruruwan magoya bayan Liverpool sun shiga tsaka mai wuya bayan soke tashin jirage uku da za su dauke su zuwa birnin Kiev don kallon wasan karshe na Gasar Cin Kofin Zakarun Turai.
Kamfanin Worldchoice Sports da ke da alhakin jigilar magoya bayan kungiyar ya ce ya kasa samun wurin da jiragen za su sauka a filin jirgin saman Boryspil a Kiev.
Kamfanin ya nemi afuwar magoya bayan kungiyar.
Matakin dai bai yi wa magoya bayan Liverpool dadi ba, wadanda suka biya fam 1,000 domin zuwa kallon wasan a Kiev, babban birnin Ukraine.
A ranar Asabar ne Liverpool za ta fafata da Real Madrid a wasan karshe na Gasar Cin Kofin Zakarun Turai.
Magoya bayan Liverpool yanzu suna kokarin bin wadansu hanyoyi domin zuwa kallon wasan.
Kamfanin Worldchoice Sports ya ce daga ranar Alhamis zai fara mayar wa magoya bayan Liverpool da kudinsu.
A sanarwar da kungiyar ta fitar game da al'amarin, Liverpool ta ce magoya bayanta kusan 1,000 ne matsalar ta shafa.
Ta ce za ta yi kokarin tattaunawa da hukumomi domin tabbatar da ganin magoya bayanta sun samu damar kallon wasan a Kiev.
Wasu daga cikin magoya bayan sun bayyana bacin ransu a shafin Twitter.
Wasu daga cikinsun sun ce za su yanki tikitin jirgi zuwa Romania daga nan su bi ta mota, tsawon sa'o'i 10 zuwa Ukraine.

0 Comments: