Headlines
Loading...
Rasuwar Sheikh Isyaka Rabiu babban rashi ne- Sheikh Dahiru Bauchi

Rasuwar Sheikh Isyaka Rabiu babban rashi ne- Sheikh Dahiru Bauchi


Sheikh Dahiru Usman Bauchi da aike da sakon ta’aziyarsa da dumbin mahaddata Alqur’ani da mabiya darikar Tijjaniya Faida Ibrahimiyya da al’ummar Jihar Kano da masarautar Kano da malaman kasashen Moroko da Senegal bisa wannan rashi na babban malami.

“Mu mahaddata Qur’ani mun yi rashi. Mu ‘yan Tijjaniya mun yi rashi. Manyan attajirai ma sun yi rashi.

“Muna alfahari da shi. Malami ne da zai yi darasu da la’asar, ya ja sallar Magriba, sannan ya bude wazifa, kuma da safe ya tafi kasuwa, Mutumin kirki ne, kuma bawan Allah wanda ya yi addini hidima. Allah Ya gafarta masa.

“Ya gina masallatai da makarantu, kuma ya tallafawa almajirai da malamai a lokacin rayuwarsa. Muna addu’ar Allah Ya yafe masa kura-kuransa Ya kuma albarkaci abin da ya bari.”  

0 Comments: