Headlines
Loading...
Matashi ya kona yara 8 da tafasasshen mai wurin sayen kosai

Matashi ya kona yara 8 da tafasasshen mai wurin sayen kosai

A shekaranjiya Laraba da misalin karfe 7:40 na safe wani matashi ya kona wadansu yara takwas da suka je sayen kosai da doya don karya kumallo da tafasasshen mai lokacin da matashin ya doke kaskon tuyar da takaliminsa. Matashin mai suna Rabi’u Uba yana jayayya ne da mai kosan mai suna Hajara Ahmad a Unguwar Malafa da ke birnin Kano bisa zarginta da rashin share wurin da take sana’arta.

Majiyarmu ta ce sai Rabi’u ya dauki takalmi ya doki kwanon tuyar inda tafasasshen man ya fallatsa a jikin yaran da ke kewaye da mai kosan. Hakan ya jawo suka samu raunukan kuna a jikinsu, nan take aka kai yaran Asibitin kwararru na Murtala kafin daga bisani a sallame su.

Wani ganau da ya nemi a boye sunansa ya shaida wa Aminiya cewa, “Matashin yana fitowa daga gidansu sai ya kalli wurin da mai kosan ke sana’arta ya ga an tara kasa don haka sai ya fara zaginta cewa ba ta share wurin ba, duk da cewa ba a kofar gidansu take ba. Jin zafin zagin da yake yi mata ne ya sa ta shiga ramawa hakan ya sa ya dauki takalmi ya doke kwanon tuyar da ke kan wuta. Nan take tafasasshen man da ke ciki ya kokkona yaran da ke wurin. Muna zaton dai sai da ya yi shaye-shayensa sannan ya aikata hakan, da yake kowa ya san yana shaye-shayen miyagun kwayoyi,” inji majiyar.

Yaran da tsautsayin ya auka musu sun hada da Hasiya Auwal ’yar shekara 4 da Usman Yahya mai shekara 15 da Nura Auwal mai shekara 5 da A’isha Banufe mai shekara 7 da Abbas Bala mai shekara 9 da Ali Isa mai shekara 9 da Yusha’u Umar mai shekara 14 da kuma Auwalu Kabiru mai shekara 17.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano SP Magaji Musa Majiya ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce tuni rundunarsu ta kama wanda ake zargi da aika-aikar kuma za su gurfanar da shi gaban shari’a.  

0 Comments: