Headlines
Loading...
Gasar Rubutu ta Mata ta BBC Hausa 2018

Gasar Rubutu ta Mata ta BBC Hausa 2018

Gasar Rubutu ta Mata ta BBC Hausa 2018

A shekarar 2016 Aisha Muhammad Sabitu ce ta ciri tuta, yayin da Maimuna Idris Sani Beli ta bayar da mamaki a 2017.
Mai yiwuwa lokaci ne da tauraruwarki za ta haska a bana; don haka, hanzarta ki kago, ki tsaro, ki kuma rubuto naki labarin don shiga Gasar Rubutu ta Mata ta BBC Hausa, wato Hikayata, ta bana.
Don shiga gasar, rubuta labarin da bai kasa kalma 1,000 ba, kuma bai haura kalma 1,500 ba, tun daga ranar 8 ga watan Mayu har zuwa ranar 8 ga watan Yulin 2018.
Idan kika yi nasara, za ki samu kyautar kudi da lambar yabo, yayin wani bikin bayar da kyauta da za a yi a Abuja.
Shin kina da labari mai kayatarwa, kuma kina da burin shiga sahun taurarin Hikayata? Za ki iya shiga gasar ta hanyar aiko da naki labarin ta email zuwa [email protected] ko kuma ta hanyar cike fom din shiga gasar da ke kasa.

0 Comments: