Headlines
Loading...
An kirkiro sinadari mai narkar da roba a cikin dan Adam

An kirkiro sinadari mai narkar da roba a cikin dan Adam

An kirkiro sinadari mai narkar da roba a cikin dan Adam
Masana kimiyya a Amurka da Burtaniya sun kirkiro wani sinadari mai iya narkar da roba a cikin dan adam, inda ake sa ran wannan sinadari zai taimaka wajen yaki da gurbatar muhalli da ake samu saboda yawan tara roba a muhallai.
Masu bincike a jami'ar Portsmouth da ke aiki da masu nazari a Amurka da Brazil ne suka gano cewar tsarin narkar da abinci a cikin dan adam na dogaro ne a kan wani sinadari wanda su ka yi bincike a kai sannan suka inganta shi domin ya yi aiki fiye da yadda yake yi kafin binciken.
Gwaje-gwaje sun nuna cewa sinadarin na iya narkar da daya daga cikin nau'o'i na roba mafi shahara mai suna Polyethylene terephthalate- PET, wanda a ka fi amfani da shi a masana'antun abinci da abubuwan sha.
Wannan nau'in na roba dai wanda ake iya sake amfani da shi ne, sai dai idan aka zubar da shi a shara, ya kan dade bai lalace ba.

0 Comments: