Headlines
Loading...
 Ana Zargin Dakarun Afghanistan da Kashe Fararen Hula 9

Ana Zargin Dakarun Afghanistan da Kashe Fararen Hula 9

Ana zargin dakarun tsaron Afghanistan na musamman, da dakarun Amurka ke marawa baya da kisan fararen hula guda 9 da kuma raunana wasu su 8 a gabashin lardin Nangarhar, wadanda ga dukan alamu anyi zaton mayakan ISIS ne.

Wani mai magana da yawun gwamnatin lardin ya fadawa muryar Amurka yau Talata cewa yawancin wadanda harin da aka kai da tsakar dare a gundumar Chaprahar ya shafa iyalin shugaban majalisar dattawan Afghanistan ne.

Attaullah Khogyani ya fadi cewa wani kwamandan ‘yan sanda da wasu dogarawansa guda biyu na cikin wadanda aka kashe. Ya kuma kara da cewa an fara bincike don gano dalilin da ya sa jami’an tsaron na musamman kai farmakin na tsakar dare a wurin ba tare da hadin guiwar jami’an tsaron yankin ba.

Gwamnatin Afghanistan ta tsakiya ta dai ce ta tura wakilai don su gudanar da bincike akan mummunan harin da aka kai, a cewar Khogyani. Dakarun tsaron Amurka dake Afghanistan ba su ce komai ba gameda harin.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane fiye da 10,000 aka kashe ko aka jikkata a shekarar 2017 kuma adadin wadanda ke mutuwa na karuwa a wannan shekarar.


0 Comments: