Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya amince da kwarewar sabbin manyan sakatarori 11 a jiharsa hakan ya sanya ya amince da kara musu girma.
Sakatarorin dai suna cikin wadanda gwamnatin jihar ta umarce su da su rubuta jarabawa domin nuna cancantarsu ta zama Manyan Sakatarori a jihar.
Gwamna ya nuna godiyarsa ga shugban ma’aikatan jihar wajen tantance Sakatarorin.
Ya ce yana gani a duk kasar nan babu gwamnatin da ta yi hakan wajen zaben Manyan Sakatarorin kamar yadda aka yi a jiharsa.
Ya yi kira ga wadanda aka zaba da su zage dantse wajen yin aiki domin ci gaban jihar.
Shugaban Ma’aikatan Jihar Adamawa, Dokta Edgar Amos ya ce wannan irin zaben da aka yi ba a taba yin irinsa ba, domin zabe ne da aka gudanar ta hanyar zana jarabawa, wanda kuma shi ne irinsa na farko a tarihin jihar.
Amos ya kara da cewa wannan ci gaban da aka samu zai taimaka sosai wajen tafiyar da harkokin gwamnati a jihar.
Wasu daga cikin Sakatarorin da suka samu nasara sun hada da Dorothy Augustine da Gajere Japhet da Saso Benson da kuma Felicia Jatau.
Sannan akwai Bello Hamman- Diram da Isuwa Misali da Ali Belhour da Aminu Hamman- Bello da Zainab Adamu da Usman Hamman-Mapeo da kuma Mohammed Dabo.
0 Comments: