Headlines
Loading...
An Kwashe Gadajen Cibiyar COVID-19 A Jihar Taraba

An Kwashe Gadajen Cibiyar COVID-19 A Jihar Taraba

An Kwashe Gadajen Cibiyar COVID-19 A Jihar Taraba

Wasu jerin tsagerum matasa sun kwashe gadaje da katifu da sauran kayan aiki a cibiyar kula da masu cutar COVID-19 ta Jihar Taraba a yau litinin. 

Dubban matasa sun mamaye cibiyar da ke sansayin horas da masu yi wa kasa hidima a hanyar Wukari-Jalingo suka kwashe gadajen da yawansu ya kai 200.

Tawagar hadin gwiwar ’yan sanda da sojoji ta isa wurin domin hana kwashe kayan amma ta kasa shawo kan ’yan daban.

An rika ganin matasa dauke da kayayyakin a kawunsa, wasu a kan ababen hawa suna kaiwa kauyukan da ke makwabtaka da garin Jalingo.

Wani shaida ya tabbatar wa Aminiya cewa yanzu cibiyar ba ta da komai saboda ’yan daban sun wawushe duk abin da ke cikin wurin.

0 Comments: