Rahotanni
Ba Gwamnatin Tarayya Bace Ta Bamu Kayan Da Aka Yi Warwasonsa - Fintiri
Biyo bayan warwason da jama'a ke yi a wuraren ajiye kayayyakin abinci na gwamnati, yanzu haka gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri ya yiwa al'umman jihar jawabi tare da kafa dokar hana fita na tsawon awanin ashirin da hudu.
To sai dai kuma duk da dokar hana fitan da ta soma aiki da misalin karfe uku na ranar Jiya Lahadi, jama'a musamman matasa sun yi biris tare da kai farmakin wasoso a wasu wuraren da aka ajiye kayayyakin, har cikin dare. Lamarin ba a fadar jihar kadai ya tsaya ba har da wasu kananan hukumomi da suka hada da Numan.
Kakakin rundunan yan sandan jihar Adamawa, DSP Suleiman Yahya Nguroje ya tabbatar mana da batun wasoson. Ya ce zasu jibge jami’an ‘yan sanda a wuraren dake bukatar cikakken tsaro, ya kuma ce hukumar ‘yan sanda na iya kokarinta ta dakile wannan fitina da ta taso.
Kamar Adamawa a Taraba ma an samu irin wannan tirmitsitsin inda shugabanin Al'umma ke kira da akai zuciya nesa.
Senata Aisha Jummai Alhassan tsohuwar ministar ma'aikatar harkokin mata ta yi kira ga matasa su yi hakuri da wannan al’amari saboda abin da zaman lafiya bai bayar ba, rashin zaman lafiya ba zai kawo shi ba. Ta ce tun da gwamnonin jihohi sun yi masu alkawari kana shugaban kasa ya rusa SARS, yakamata su yi hakuri kada wannan abu ya janyo babbar fitina a cikin kasar.
saurari rahoton Ibrahim Abdulaziz cikin sauti:
0 Comments: