Headlines
Loading...
Kayan da Buhari ya hana CBN ba da kudaden waje don shigo da su Najeriya

Kayan da Buhari ya hana CBN ba da kudaden waje don shigo da su Najeriya

Kayan da Buhari ya hana CBN ba da kudaden waje don shigo da su Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake nanata umarnin da ya bayar ga Babban Bankin ƙasar kan cewa kada ya kuskura ya bayar da canjin dala ko kuɗin kasashen waje domin shigo da kayan abinci ko kuma takin zamani.




A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasar ta fitar, Shugaban Buhari ya shaida wa Babban Bankin Najeriya cewa "kada a bayar da ko kwabo daga cikin kuɗin kasa domin shigo da abinci ko kuma taki".


A wani taro da aka gudanar kan samar da abinci a ƙasar da aka yi a Abuja, ya ce zai bayar da wannan umarni a rubuce kan cewa kada a fitar da kuɗi domin sayen abinci.
Me ya sa shugaban ya ɗauki wannan mataki?






Shugaban ya daɗe yana cewa zai haɓaka samar da abinci a cikin ƙasar. Shugaban yana da yaƙinin cewa komawa gona na daga cikin hanyoyin da za a bi domin kawo ƙarshen matsalar ƙarancin abinci da kuma rashin aikin yi a ƙasar.


A yayin taron, shugaban ya sake nanata alƙwarin da gwamnatinsa ta yi na wadata da ƙasar da abinci.


A ƙoƙarin gwamnatinsa na ƙara haɓaka ƙananan manoma, shugaban ya bayyana cewa:


"Daga kamfanonin takin zamani guda uku da muke da su a Najeriya a baya, a yanzu muna da 33 da ke aiki. Ba za mu biya kwabo ɗaya ba daga baitul malin ƙasa domin shigo da taki. Za mu taimaka wa na ƙasar mu."




Shugaban ya kuma bayar da umarni kan cewa kamfanonin da ke samar da takin zamanin su rinƙa kai wa gwamnatocin jihohi takin da suka samar kai tsaye domin gudun masu karkatar da takin, kuma hakan zai sa ba zai kai ga manoma ba kan farashi mai rahusa.


Shugaban ya kuma bayar da shawara ga duk wani ɗan kasuwa mai zaman kansa da ke da sha'awar shiga da abinci ƙasar da ya je ya nemo canjin dala a wani wuri amma ba a Babban Bankin Najeriya ba.
Jerin kayayyakin da Najeriya ba za ta bayar da canjin kuɗi ba domin shiga da su ƙasar




A shekarar 2015, Babban Bankin Najeriya ya fitar da jadawalin kayayyakin da ba za su bayar da canjin kuɗi ba domin shiga da su, kuma sun yi hakan ne domin ƙarfafa gwiwar manoma.


Tsarin da suka fitar ya ce masu shiga da irin waɗannan kayayyaki Najeriya ba za su iya samun canjin kuɗi ba daga babban banki, sai dai su nemi kuɗin daga kasuwar bayan fage domin shiga da kayayyakin.
  • Shinkafa
  • Siminti
  • Man bota
  • Man ja da man gyaɗa
  • Nama
  • Kayan salak
  • Kaji da talotalo da ƙwai
  • Kifin gwangwani
  • Kwanon rufi
  • Baro
  • Akwatunan ƙarfe
  • Rodi
  • Ƙusa
  • Katako
  • Ƙofofi
  • Gilas
  • Kayan kitchen
  • tamfofi
  • Kayan sawa
  • Sabulu da kayan shafa
  • Tumatir

0 Comments: