Headlines
Loading...
Zamfara : Yadda masu garkuwa da mutane suka sace alkalai biyu

Zamfara : Yadda masu garkuwa da mutane suka sace alkalai biyu


Wasu 'yan bindiga sun sace wasu alkalai biyu na kotun shari'ar musulunci a jihar Zamfara, yayin da suke komawa gida bayan wani bulaguron karo ilimi da suka yi.

Alkalan sun hadar da Malam Shafi'i Ibrahim Jangebe, da kuma Malam Sabi'u AbdulLahi.

Lamarin ya faru ne a tsakanin kananan hukumomin Jibiya da Zurmi, lokacin da alkalan ke kan hanyarsu ta komawa gida a mota.

Barista Bello Galadi, lauya ne mai zaman kansa, kuma tsohon shugaban kungiyar lauyoyi ta Najeriya reshen jihar Zamfara, ya shaida wa BBC cewa, wadannan alkalai da aka sace dalibai ne da ke karin karatu a wata makaranta da ake cewa Al-nahda International da ke Yamai a Jamhuriyar Nijar.

Lauyan ya ce,"A yanzu ana cikin juyayi na sace alkalan kasancewar ba a san halin da suke ciki ba, amma kuma mun samu labarin cewa wadanda suka sace su sun tuntubi iyalan daya daga cikinsu".

Ya ce kodayake har kawo yanzu bamu samu wani sahihin labari daga iyalan wanda aka tuntubar ba.

Barista Bello, ya ce yanzu abin da ake kai shi ne suna sauraron suji ko masu garkuwa da mutanen sun bukaci a basu kudin fansa, kodayake iyalan alkalin da aka tuntuba sun yi magana dashi ya kuma nuna musu yana cikin yanayi damuwa har iyalan nasa sun fahimci hakan.

Lauyan ya ce,"Mu yanzu a matsayinmu na abokan aikin wadannan mutane abin da muke shi ne muga mun tattauna da jami'an tsaro aga yadda za a yi a ceto wadannan alkalai".

A Najeriya matsalar tsaro ta yin garkuwa da jama'a da kuma yi masu kisan ba gaira ba dalili a yankin arewacin kasar, musamman a arewa maso yamma da suka shafi jihohin Zamfara da Katsina da kuma Kaduna na ci gaba da ta'azzara.

Wannan lamari dai ya kasance wani yanayi na Lahaula wa lakuwata a jihar Zamfara, sai dai a yanzu an dan samu sauki, sai dai a baya kusan a kowace rana sai an halaka mutane da yawa tare da asarar dukiyoyi.

0 Comments: