Headlines
Loading...
Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Shugaban Kasa: Ya Shugaba, Me Ka Ke Tsoro Ne?

Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Shugaban Kasa: Ya Shugaba, Me Ka Ke Tsoro Ne?Ya na cin zaben kujerar sanatan tsakiya a jihar Kogi ya fara kitsa makarkashiyarsa. Me ka ke tsammani daga mutumin da ya yi wa mahaifinsa makirci irin na siyasa? Sanin cewa sun goya ma ka baya wajen darewa mulkin kasar nan a shekarar 2015, Sanata Bukola Saraki da mukarrabansa sun kwana da sanin wane irin mutum ne kai, don haka sun shiga APC da shirinsu da kuma manufa. Gungun mutane ne wadanda sun fito daga jam’iyya mafi daurewa rashawa da cin hanci a tarihin siyasar kasar nan, don haka kudurinsu bai wuce na kare kansu daga barazanar da ka ke wakilta ba ta kare hakkin talaka da dakile rashawa da cin hanci. Sun gane cewa hanya daya da za su iya tsira cikin mulkinka shi ne hade kai da kwatar matsayi da zai iya ba su kariya. Wannan matsayi shi ne na shugaban majalisar dattijai. Sun yi gamon katar kasancewar ka zabi bin tsari na bawa kowanne bangaren masu mulki damar cin gashin kansa, inda ka zabi barin jam’iyyar APC ta shiga tsakani wajen zabo wanda zai dare wannan mahimmiyar kujera.

 Wannnan shi ne mafi girman kuskure da ka yi, domin yayin da su ka yaudare ka zuwa babban dakin taro na kasa-kasa da ke Abuja, tuni sun yi ma ka juyin mulki. Juyin mulki ma na tunda sun kaucewa bin tsarin jam’iyya wanda ya ba su kujerunsu su ka nada Bukola Saraki ba sahalewarka ballantana ta jam’iyya. Ka kawar da kai daga wannan zagon kasa, watakila domin tsoron kada a ce ka na mulkin kama-karya da kuma burinka na ganin ka jaddada doka da oda. 

Amma wannan ne kuskure mafi girma da ka yi shigowar ka mulki, kuma kuren da tun daga wannan rana kawo yanzu kai da talakawan kasar nan ke biya. Bari na kawo ma ka wasu daga cikin hujjojin da su ka sa na fadi haka. Lokacin da a ka fara maganar shari’ar Bukola Saraki a kotun da’ar ma’aikata, a rana ta farko ya sami rakiyar ’yan majalisa 83 daga cikin 103 da ke majalisar dattijai. Wadannan sanatoci sun yi dango domin kare rashawa da nuna su na tare da shi kasancewar kusan dukansu ja-ya-fado ne ja-ya-dauka. 

Da akwai kyautar majalisa mafi rashin kima a duniya na tabbatar da wannan majalisa ta takwas ta lashe gasar. Sakamakon alkalin ya nuna da gaske zai yi shari’ar, dattawan naka sai da su ka gayyace shi zaurensu. Bayan nan, hukumar kwastam ta kama motoci na alfarma wadanda ba a biya mu su haraji ba na shugaban majalisa, abinda ya sa majalisar ta gayyato shugaban kwastam, Hamid Ali, zuwa zaurenta, don nuna kin jinin yadda ya ke ayyukansa na ba-sani-ba-sabo. Sannan su ka matsa sai ya saka kayan aikin kwastam zai shiga zauren. Hamid Ali fa tsohon janar ne, wanda ya yi ritaya kuma mukaminsa ya fi na shugaban kwastam! Ina dalilin sai ya saka kayan sarki? 

Yayin da EFCC ta karkade fayil-fayil na sanataoci da a ke zargi kuma a ka gurfanar a gaban kotu, ciki har da shugaban majalisar, sai kawai su ka kada kugen yaki da shugaban EFCC, Ibrahim Magu, da kiraye-kirayen lallai sai ka cire shi, amma ka yi kememe, wanda sakamakon hakan su ka ki tabbatar da shi a mukaminsa a karo biyu da ya je gabansu. Na tuna cewa ba su bar kansu ba, domin daya daga cikin ’yan gaba-gaba wajen kitsa wancan juyin mulki da su ka yi ma ka, wato Ali Ndume, wanda a baya dan lelen saraki ne, amma sai ga shi sun cire shi daga mukaminsa sun dakatar da shi daga majalisa, saboda ya ja da Sarakin (Ina ganin alhaki ne ya kama shi ko?) Rigima tsakaninsu da kai ta dauki sabon salo a lokacin da ’yan sanda su ka nemi Dino Melaye ya kai kansa gabansu, saboda zarge-zarge da wasu daga cikin yaran da ya ke bawa makamai su ka fada hannun ’yan sanda. 

Dino ya ki amsa gayyatar har sai da ta kai sun cafke shi kuma ya tafka abin kunya da ya zubar da martabar majalisar dattijai da ma kasarmu gabadaya, domin nuna halayya tamkar irin ta ’yan dabar da su ka ce ya na da hannu a ayyukansu, sai ga shi ya nemi tserewa daga motar ’yan sanda lokacin da ta ke tafiya a kan titi. Kai shi kotu da kuma tsare shi a kurkuku ya jefa tsoro a zukatan su Bukola ganin cewa idan ka na sanata ba ka fi karfin doka ba. An kitsa wani makircin na kutsawa cikin majalisa da wasu ’yan daba yadda har su ka karbe sandar majalisa su ka fita da ita duk da cewa ginin majalisa na cikin wurare mafiya tsaro a fadin kasar nan, domin sai ka na da gayyata daga cikinta ko ka na aiki a ciki, sannan za ka iya shiga cikin ginin. Ina ganin an so a cigaba da kawo tsaiko ne a majalisa domin kada su sami damar sahale kasafin kudi da ke gabansu tsawon wata shida, don makarkashiya ga gwamnatinka. An yi fashi da makami mafi muni a tarihin Najeriya a garin Offa da rana tsaka, inda barayin su ka hallaka ’yan sanda tara da mutane sama da 38 ciki har da mace mai ciki a bankuna shida. Ashe wadannan gungun ’yan fashi yaran siyasa ne na Saraki, kuma bayan kwana biyu kacal da aika-aikar sai ga shi an gan su da Sarakin sun je gidan wani basarake yin jaje, saboda gwanintar makirci. A na cafke wadannan ’yan fashi da bincikarsu wanda ya sa babban sufeton ’yan sanda na kasa ya umarci a maida su Abuja. Jin haka sai gwamnan jihar Kwara ya sanar da Saraki abinda a ke ciki, shi kuwa Saraki ya na tuna abinda ya faru da Dino Melaye sai hantarsa ta duri ruwa. Nan da nan ya garzaya gabanka tare da gungun wasu ’yan majalisa, domin kai karar Sufeto Janar na ’yan sanda cewa ya na kitsa ma sa bi-ta-da-kulli. Ya’ilahi idan babu rami me ya kawo rami? Kamar yadda ka saba, ka ba su shawarar su bar doka ta yi aikinta a wanke mai gaskiya. Ciki da gaskiya kuwa ai wuka ba ta huda shi. Babban Sifeton ’yan sanda na mika wa Saraki gayyatar ya zo ya kare kansa, sai hankali ya tashi, domin ya san cewa fa alamun nesa ta zo kusa, don haka a nasa haukan gani ya ke mafita guda daya ta rage ma sa, wato ya kawo maganar a tsige ka. Watakila ya zunguro tsuliyar dodo, dodon da kuma zai hadiye shi da gungunsa, domin abinda ya yi tamkar kada kugen yaki ne a kan ’yan Najeriya. Kada mu manta nan ba da dadewa ba sanatoci da ’yan majalisar wakilai su ka hargitse lokacin da hukumar zabe ta fitar da jaddawalin zaben badi, kuma hantarsu ta duri ruwa, su ka kai gauro su ka kai mari, don ganin an canza jadawalin, amma su ka kasa samun yawan kuri’ar da za su iyi yin watsi da kudurin. Shin wadannan ne za su iya samun kuri’ar tsige ka? 

Abin dariya, yaro ya tsinci hakori! Ya Mai Girma Shugaban Kasa, na fahinci hikimarka ta barin tsarin doka ta yi aiki, domin idan hakan ya samu, ko ba ka nan, tsarin zai dore kuma a yanzu ma mun ga nasarar hakan, don kwanan nan mu ka ga kotu  ta tasa keyar Jolly Nyame kurkuku bayan fadi-tashi na kimanin shekaru 11. Sannu a hankali tsofaffin gwamnoni irinsu Shema, Shekarau, Lamido, Yero, Jang, Dariye, Goje, Kalu, Muazu da sauransu, za mu ziyarce su a kurkuku da gudunmuwar garin kwaki! 

To, amma duk da haka akwai lokaci fa na kawar da kai, akwai kuma lokaci na fuskantar abokin gaba, musamman idan da kansa ya buga kugen yaki. Na san a matsayinka na tsohon janar wanda ya jagoranci yaki ka san haka tun kafin a haife ni. Ba na manta kokarin halaka ka da makiya su ka yi, sai da ka shafe kusan shekara ka na jiyya, amma cikin hikimar Allah da addu’o’i da ka sha daga sassa na duniya Allah ya karba ya dawo ma na da kai har ka fi jiya kwari. 

Tun dawowar ka mu ke tsammanin tunda ka je bakin rami ka dawo, za ka zo ka fafari azzalumai ka garkame ma na su a kurkuku. Kash! amma sai ka ki. To, amma tunda yanzu su Bukola sun kalubalance ka gaba-da-gaba, mu na fatan ba za ka yi kasa a gwiwa ba. Wannan majalisa ta Takwas ba a taba mai muninta ba kuma tun da ta shigo ba ka jin komai daga cikinta sai yaki da gaskiya, saboda ba da Bukola Saraki kabai a ke yaki ba; shi ne dai jagora mai wakiltar dandazonsu. Yanzu dama ta samu, an sami shaidu kwarara na tuhumarsa. Don haka matukar ba a bincike shi an yanke ma sa hukunci ba, to yaki da rashawa da cin hanci da karya dokokin kasa ya yi nasara a kanka da kasarmu!


0 Comments: