Headlines
Loading...
Dubban mutane na son a hukunta Sergio Ramos kan Mo Salah

Dubban mutane na son a hukunta Sergio Ramos kan Mo Salah

Dubban mutane na son a hukunta Sergio Ramos kan Mo Salah
Ana cigaba da nuna goyon baya ga wata takardar kara ta intanet da ke neman a hukunta Sergio Ramos kan cewar ya ji wa Mohamed Salah ciwo da gangan.

An kai karar Sergio Ramos kan cewar da gangan ya yi wa Mo Salah keta a wasan karshe na gasar zakarun Turai da aka buga tsakanin Real Madrid da Liverpool.

Kuma a lokacin da ake wallafa wannan labarin mutum 314,891 ne suka nuna goyon baya ga karar da ke neman a hukunta Ramos da aka wallafa a shafin koke na intanet, petition.org.

Kawo yanzu dai hukumar kwallon kafa ta Turai, Uefa, da ake naman ta hukunta Ramos ba ta ce komai game da karar ba.
Tun ranar da lamarin ya faru ne dai Sergio Ramos ya yi wa Mohamed Salah fatan samun sauki da wuri. A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Ramos ya yi wa Salah fatan alkhairi.

  • El fútbol te enseña la cara más dulce a veces y la más amarga otras. Ante todo somos compañeros. Pronta recuperación, Salah. El futuro te espera.||Sometimes football shows you it's good side and other times the bad. Above all, we are fellow pros. @MoSalah 
Shi kuma Mohamed Salah ya ce yana fatan cewa zai samu buga gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a watan gobe.

A wani sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter, dan wasan na Masar da ke taka leda a Liverpool, ya gode wa masoyansa a fadin duniya, yana mai shan alwashin burge su.


It was a very tough night, but I'm a fighter. Despite the odds, I'm confident that I'll be in Russia to make you all proud. Your love and support will give me the strength I need.

0 Comments: