Labaran Yau
Kungiyoyin Kare Hakkin Jama’a A Nijar Sun Yiwa ‘Yan Siyasar Kasar Kashedi
Kungiyoyin kare hakkin jama’a a Jamhuriyar Nijar sun jawo hankalin
‘yan siyasar kasar da su sasanta da juna domin kada su jefa kasar cikin
rikicin siyasa da ba zai tsinana wa kowa komi ba illa tashin hankali
WASHINGTON DC —
Yadda kowane bangaren siyasar kasar Nijar ya dage akan bakarsa akan batun zabubbuka ya damu wasu ‘yan kasar. Ja-in-ja da ‘yan siyasar keyi ya sa kungiyoyin kare hakkin jama’a,
suka fara jawo hankalinsu da su sasanta da junansu ta yadda za’a shirya
zabubbukan cikin lumana.Dambashi Son Allah shugaban wata kungiyar kare hakkin jama’a ya ce ‘yan siyasa dake mulkin kasar sun dage babu canji akan hukumar zaben yayinda ‘yan adawa suke cewa ba zata sabu ba, dole sai an yiwa hukumar zabe kwaskwarima ta yadda kowa zai samu wakilci. Ya ce dukansu sun ja daga basu damu da kasar ba alhali kuwa idan babu kasar duk wani shirin zabe ya zama a banza. Yace kowa ya sani idan aka yi tashin hankali na zabe, ya kanyi muni.
Shi kuwa Alhaji Salisu Ahmadu na wata kungiyar kawancen ya yiwa bangarorin biyu tuni akan nauyin da ya rataya a kansu domin raya mulkin Dimokradiya. Alhaji Salisu yace ‘yan siyasa basu san cewa batun zabe basu kadai ya shafa ba. Kasar nada mutane kimanin miliyan ashirin kuma kowa lamarin ya shafe shi saboda kowa nada ‘yancin y afito ya yi takara ba sai ya shiga wata jam’iyyar siyasa ba. Ya kamata a saurari kowa a samu amincewa.
Hukumar zabe ta CENI na da rawar da zata taka wajen warware kiki-kaka da ta ki ci ta ki cinyewa tsakanin bangarorin siyasar kasar a cewar shugaban kungiyar kadet. Ya shawarci hukumar zaben ta jajirce akan abubuwan da doka ta tsara domin kaucewa tarkon da ‘yan siyasa ke neman kafawa domin kawo cikas ga shirin zabukan. Ya ce ya kamata hukumar zabe ta dauki matakin sasanta ‘yan siyasa domin su komo gurbi guda. Yace kada hukumar ta yadda wani dan siyasa ya tursasata. Ta tsaya kan Gaskiya da dokokin kasa.
Ita hukumar zaben da aka kafa bayan an yiwa kundun tsarin zabe kwaskwarima, ‘yan adawa na ganinta tamkar ‘yar amshin shatar gwamnati ce lamarin da ya hanasu aikewa da nasu wakilan zuwa cikin hukumar.
Saurari rahoton Souley Barma domin jin karin bayani
0 Comments: