Headlines
Loading...
Tsoffin 'yan sabuwar PDP sun gana kan Buhari

Tsoffin 'yan sabuwar PDP sun gana kan Buhari

Tsoffin 'yan sabuwar PDP da suka hada da shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, da shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, sun yi taro kan makomarsu a jam'iyyar APC.
Wata sanarwa da Alhaji Abubakar Kawu Baraje, shugaban 'yan PDP sabuwa ya raba wa manema labarai ta ce taron ya biyo bayan wasikar koken da 'yan siyasar suka rubuta wa jam'iyyar APC mai mulki ne da kuma ganawar da shugabanninsu suka yi da jam'iyyar APC bayan wasikar.
Shugaban majalisar wakilan, ya ce a taron da aka yi domin sanar da 'yan sabuwar PDP din abin da jam'iyyar APC ta sanar da wakilan sabuwar PDP din, an kafa kwamiti daban daban.

Ya ce muhimmin makasudin kafa kwamitin shi ne ta yadda za a ceto Najeriya daga kalubale na siyasa da zamantakewa da kuma na tsaro.
Cikin wadanda suka halarci taron ne gwamnan Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da Prince Olagunsoye Oyinlola da Admiral Murtala Nyako (Rtd) da kuma Sanata Mohammad Adamu Aliero.
Har wa yau a cikin wadanda suka halarci taron akwai Sanata Danjuma Goje da Sanata John Owan Enoh da Sanata Emmanuel Andy Uba da Sanata Ibrahim Gobir da Sanata Rufai Ibrahim da Sanata Ibrahim A. Danbaba da Sanata Suleman Nazif da kuma Sanata Isa Hamma Misau.
Mahalarta taron sun hada da Sanata Muhammed Ubali Shitu da Sanata Shehu Sani da Sanata Dino Melaye da Sanata Suleiman O. Hunkuyi da Sanata Shaaba Lafiagi da Sanata Bala Ibn Na'Allah da Sanata David Umaru da Sanata Barnabas Gemade da kuma Alh. Abubakar K. Baraje wanda shi ne tsohon shugaban sabuwar PDP din.


0 Comments: